Rabiu Ali Indabawa" />

An Kama ’Yan Bindiga 17 Da Suka Yi Garkuwa Da Mutane 23 A Taraba

Babban Sufeton ’Yan Sanda

Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan Jihar Benue Laftanal Kanal Paul Hemba (Mai ritaya) a ranar Talata ya ce an kama barayi 17 da suka sace mutane 23 a Jihar Taraba. Jaridar The Nation, ta tattaro cewa a ranar 27 ga Janairun 2021, wasu masu aikata laifuka wadanda suke da alaka da marigayi Terwase Akwaza, da aka fi da da suna Gana, sun sace mutane 23 a kan hanyar Wukari-Takum. Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan Jihar Benue Laftanal Kanal Paul Hemba (Mai ritaya) shi ya sanar da haka a ranar da ake holing barayin, ya ce an kama barayi 17 a kan laifin sace mutum 23 a Jihar Taraba.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa a ranar 27 ga Janairun 2021, wasu masu aikata laifuka wadanda suke da alaka da marigayi Terwase Akwaza, shahararren dan fashi da makami da satar mutane da aka fi sani da Gana sun sace mutane 23 a kan hanyar Wukari-Takum.
Da yake jawabi ga manema labarai a gidan Gwamnati da ke Makurdi, Kanar Hemba ya ce shirin da aka yi na satar shi ne don haifar da rikicin kabilanci tsakanin kabilun Tib da Jukum don karkatar da hankalin jami’an tsaro a kansu.
Ya ce, rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Whirl Stroke’, Bataliyar Sojoji ta Musamman ta 72, Batalion Batum 93 da Takum da ‘Yan Sanda daga Takum sun kai farmaki maboyar wadanda ake zargin inda aka ajiye wadanda abin ya shafa a yankin Ajon, Igbudu da Tor Donga. Tawagar ta kubutar da mutane 19 daga cikin 23 da aka sace, kuma tana neman sauran hudun. Sojojin sun cafke wasu ‘yan fashi 17 da ke da alaka da satar a yayin sumamen a sassa daban-daban na karamar Hukumar Ala. Mai bai wa shugaban shawara kan harkar tsaro ya ce wadanda ake zargin, DSS sun yi musu bayani a bataliya ta 93 da ke karamar Hukumar Takum.

Exit mobile version