An Kama ‘Yan Fashin Da Suka Addabi Cikin Garin Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Katsina, Karkashin Jagorancin Kwamishinan Yansanda Sanusi Buba ta yo nasarar cafke wasu Yan fashi da makami a cikin garin Katsina. Wadanda aka Kama akwai Isah Ibrahim, dan shekara 30, da ke zaune a unguwar Tudun Yanlahidda cikin garin Katsina da Kuma Lawal Bilal, Dan Shekaru 25, mazaunin unguwar Kofar Marusa.
A Cigaba da binciken da rundunar ke yi, an Kama su da karamar bindiga, sun amsa laifin su, Kuma sun ce akwai wasu mutane biyu da suke tare Kuma tare suka aikata laifin, amma sun ruga.

Exit mobile version