An Kama ‘Yan Nijeriya Bisa Laifin Garkuwa Da Mutane A Ghana

‘Yan Sanda a kasar Ghana sun sanar da kama wasu ‘yan Nijeriya guda uku cikin mutanen da ake zargi da sace wasu ‘yan kasar Kanada guda biyu da aka yi garkuwa da su a baya. Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kama ‘yan Nijeriya da aikata irin wannan laifi a kasar ta Ghana, Haka zalika a watan Afrilun da ya gabata, an sace wani dan kasar Indiya a birnin Kumasi, wanda aka nemi makudan kudade kafin sakin sa, sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo ba jami’an tsaron kasar suka yi nasarar ceto shi.

Wata kididdiga ta nuna cewa, a duk shekara sama da ‘yan kasashen ketare miliyan daya da dubu 300 ne ke ziyartar kasar Ghana, akasarinsu domin yawan shakatawa da kuma kasuwanci.

Ambassada Ibrahim Kazaure, tsohon Jakadan Nijeriya a Saudi Arebiya, ya bayyana damuwa kan yadda matsalar ke iya shafar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Exit mobile version