Rabiu Ali Indabawa" />

An Kammala Aikin Masallaci Mafi Girma A Asiya

An kammala ginin masallacin da shi ne ya fi ko wanne girma a Asiya ta tsakiya wanda Ma’aikatar Addinai Ta Turkiyya ta dauki nauyin aikinsa a Bishkek babban birnin Kazakistan. A shekarar 2012 aka fara ginin inda kuma aka yi sa cikin tsarin ginin Daular Usmaniyya.
Masallacin an yi sa ne a gabashin babban birnin inda ya ke da girman ma’aunar metre cube dubu 7 da 500.
Kimanin mutane dubu 20 ne za su iya ibada a lokaci guda a cikin harabar masallacin. Filin masallacin zai iya daukar motoci 500 a lokaci guda inda kuma yake da makarantar kur’ani da gidan cin abinci da ofishin ma’aikata.
Ratotanni sun nuna cewa yanzu haka ana goge-goge ne kafin a bude masallacin. A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa kaso 70 cikin 100 na wadanda suka yi aiki a wurin ‘yan kasar ne inda aka ce an ji dadin ganin cewa Turkiyya ta samawa ‘yan kasar aiki yi.

Exit mobile version