An Kammala Gasar Bidiyo Da Hotuna Ta “Sin Da Afirka” Ta Shekarar 2021 Cikin Nasara

Daga CRI Hausa,

An sanar da sakamakon gasar bidiyo da hotuna ta “Sin da Afirka” ta shekarar 2021, mai taken “Dora mihimmanci kan zumunci a tsakanin Sin da Afirka, da kafa kyakkyawar makoma tare” a jiya Alhamis.
Michael Mubaiwa daga kasar Zimbabwe ya zamo na 1 a fannin bidiyo, yayin da a nasa bangaren ma Huang Shiyong, likitan kasar Sin dake aikin ba da tallafi a Afirka, ya zamo na 1 a fannin hotuna.

A cikin jawabinsa, jakadan Zimbabwe a kasar Sin Dr. Martin Chedondo, ya bayyana cewa, wannan gasar ba gasa ce kadai ba, har ma wani gagarumin biki ne na murnar abota tsakanin Sin da Afirka, da nuna al’adu masu tarin yawa.

Jakadan ya kara da cewa, “Kamar yadda ake magana, hoto daya ya fi kalmomi dubu. Ya ce “A cikin yanayin da muke ciki na tinkarar annobar COVID-19, babu wata hanyar da ta fi bidiyo da hotuna wajen nuna zumunci a tsakaninmu, da more fasahohin da muka samu a fannin al’adu.” (Mai fassara: Bilkisu)

Exit mobile version