An Kammala Kacici-Kacicin da CITAD Ta Shirya Ga Daliban Jihar Kano

Daga Abba Gwale,

Makarantar sakandiren kimiyya ta Dawakin Tofa ta lashe gasar kacici-kacici ta na’ura mai kwakwalwa da Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD ta shirya ta wannan shekarar.

Gasar, wadda itace karo na 20 da cibiyar take shiryawa ta gudana ne a jami’ar kimiyya da fasaha dake Wudil dake jihar Kano inda makarantu 32 dake fadin jihar Kano suka fafata sannan kuma aka fitar da wadda tayi na daya da ta biyu sannan da kuma ta uku.

Kamar yadda aka tsara gasar, makarantar da tazo ta daya ta samu kyautar computer da refurbished computer da printer da agogon bango sai makarantar da tazo ta biyu itama ta samu computer da printer da agogon bango sannan wadda tazo ta uku ta samu computer da agogon bango.

Makarantar kimiyya da fasaha ta Kano ce tazo ta biyu ya yinda makarantar gwamnati ta Tudun Wada tazo ta uku a gasar wadda ta samu halartar dalibai da dama tare da malamansu.

Suma malamai ba’a barsu a baya ba, domin an bawa malamin da yafi bajinta kyautar talabijin din bango sannan an bawa dalibai shida da suka fi nuna hazaka jakar makaranta da litattafai da kayan daukar horo na CITAD sannan duka daliban da suka fafata sun rabauta da shaidar halartar gasar.

A jawabinsa da manema labarai, Ahmad Abdullahi Yakasai, mataimakin shugaban cibiyar sannan shugaban sashin horo ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ta bunkasa ilimin na’ura mai kwakwalwa ga daliban kasar nan domin suma su goga kafada da kafada da ragowar daliban kasashen duniya.

Shima a nasa jawabin, mataimakin shugaban jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil, Dr. Tijjani Sale Bichi, ya bayyana cewa jami’ar a shirye take da ta ci gaba da bayar da gudunmawa domin samun ci gaban al’umma sannan ya ce shugaban jami’ar ya bayar da dama a duk lokacin da za ayi wannan gasa zasu bayar da wajen gabatarwa.

Cibiyar CITAD dai ta kasance cibiya daya tilo wadda ta dade tana bayar da gudunmawa ga harkokin fasahar zamani a jihar Kano da fadin kasar nan baki daya inda a koda yaushe takan shirye bita ko taron karawa juna sani ko kuma horo domin dai ganin an samu al’umma mai ilimin zamani.

Exit mobile version