Daga Abdullahi Muhd Sheka,
A ranar Asabar da ta gabata Kwamitin shirya Musabakar Alkur’ani Mai girma da aka saba kowacce Shekara ya kawo karshen Musabakar ta Bana a Jihar Kano, masubakar Wadda hukumar makarantun Islamiyya da na Tsangayu ta saba shiryawa karo na 35.
Musabakar Wadda Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dauki nauyin gudanarwa inda an samu ‘yan takara guda 300 wadanda suka shiga gasar data gudana tsakaninKananan hukumomin Jihar Kano 44.
Wadannan ‘yan takarkaru da suka fafata, Wanda daga cikinsu aka samu guda 60 da suka sami nasara kuma su ne Gwamna Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince Kuma aka ba su kyaututtuka a kowanne bangare daga na 1-5.
Wannan Gwarzon na wannan shekara ya samu kyautar Mota, kudi da kujerar Hajji, sai Gwarzuwar shekara a bangaren mata wadda itama samu mota, kudi da kujerar Hajji daga Gwamna Jihar Kano kuma Khadimul Islam.
Da yake gabatar da jawabinsa mataimakin Gwamnan Jihar Dakta Nasiru Yusif Gawuna Wanda Kuma shi ne Kwamitin da zai Jagoranci Musabakar ta kasa da za’a gudanar a Jihar Kano Nan Bada jimawaba, ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda ‘yan takarkarun suka baje kolin baiwar da Allah ya yi masu, saboda haka sai ya taya wadanda suka Samu nasarar murnar wannan nasara.
Gawuna ya Kuma bukaci wadanda za su wakilci Jihar Kano a kasar ta kasa da su kara jajircewa domin samun nasarar a gasar ta kasa dama ta duniya Baki daya.
Musabakar ta bana ta Samu kyaututtuka daga manyan ‘yan kasuwa, attajira da ‘yan majalisun Tarayya, daga cikinsu akwai wakilin karamar hukumar Tarauni a Majalisar wakilai ta tarayya Hafiz Ibrahim kawu. Kamar yadda Babban mataimaki na musamman Kan Harkokin Islamiyyu Ibrahim Inuwa Yakasai ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.