Jamil Gulma" />

An Kammala Zaben Fitar da Gwani Na Kananan Hukumomi A Kebbi

An kammala zaben fitar da gwani a cikin shirin hukumar zabe ta jihar Kebbi na zaben gama-gari na kananan hukumomi da za a gudanar ranar Asabar 26 ga Oktoba, 2019.

Wakilinmu a jihar Kebbi ya zagaya wadansu kananan hukumomi don ganin yadda ta kaya.

Dan majalisar dokoki na jihar mai wakiltar Arewa, Hon. Samaila Salihu Bui, ya ja kunnen ’yan siyasa da su cigaba da zama lafiya tsakaninsu kasancewar karamar hukumar mulki ta Arewa an san ta da zama lafiya, sannan kuma su guji duk wani abu da zai kawo tashin hankali.

Haka shi ma kantoman riko Malam Abubakar B. Umar Bunza ya gode wa Allah bisa ga samun nasarar kammala wannan zaben a cikin lumana, ya kuma yaba wa jami’an tsaro dangane da rawar da su ka taka.

Daga karshe kuma ya yaba wa gwamnati da hukumar zabe bisa ga damar da su ka bai wa wakilai su ka zabi dan takarar da jama’a ke so.

A karamar hukumar mulki ta Augie danmajalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar mulki ta Augie Honarabul Saniya bayyana cewa jam’iyyar APC daya ce manufa daya saboda haka ya yi kira ga dukkan bangarori da su hada hannu don cigaban karamar hukuma da jiha. Kamar yadda kowane musulmi ya sani komai mukaddari ne daga Allah saboda haka ya kamata a mayarda lamurra ga Allah

Babban jami’i wanda ya jagoranci gudanar da zaben a karamar hukumar mulki ta Augie Alhaji Abubakar Nayaya ya bayyana farin cikin sa bisa ga ga kammala wannan zaben cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma yabawa jami’an tsaro da yansiyasa bisa ga hadinkan da suka ba shi na ganin an kammala zaben lafiya.

Ya ce ala kulli halin a duk lokacinda mutane fiye da daya ke neman abu daya ba shakka doke wani ya samu wani Kuma ya rasa saboda haka ya yi kira ga dukkan bangarori da su hada kai a yi aiki tare su ma in Sha Allahu ba za su tashi a tutar babu ba saboda gwamnati tana da

fadi.

Malam Lauwali Yola shi ne ya sami nasarar lashe zaben fitarda gwani a karamar hukumar mulki ta Augie ya bayyana godiyarsa ga Allah sannan kuma ya yabawa jama’ar da suka bi dare suka bi rana don ganin an cimma nasara.

Ya kuma yi fatar Allah ya ba su ikon lashe zaben gamegari mai zuwa nan da makonni biyu

Alhaji Abdullahi Usman Gulma shi ne wanda ya sami nasarar lashe zaben fitarda gwani a karamar hukumar mulki ta Argungu kuma ya tattauna da manema labarai Jim kadan bayan sanarwar samun nasarar sa inda ya bayyana cewa wannan ba wata gwanintarsa ba ce ko wani kokari na sa ba illa dai nasara ce daga Allah, bayan wannan kuma ya yi kira ga sauran yantakara da suka fafata da su zo su hada kai su yi aiki tare.

Sai dai rahotanni daga wadansu kananan hukumomi ba a sami aiwatar da zaben ba ranar Assabar, saboda an tayar da jiyoyin wuya inda kuma a wadansu kananan hukumomi jami’an zaben ba su isa cikin lokaci ba saboda haka har ya zuwa lokacin hada rahoton nan ba a kammala ba duk da ya ke kusan mafi yawancin kananan hukumomi an kammala inda a mafi yawancin wurare sababbin ‘yan takara a ka zaba.

Exit mobile version