An Kara Farashin Wutar Lantarki

A Ranar larabar data gabata ne, hukumar duba wutan lantarki ta kasa ta yi shelar ta tabbatar da karin farashin wutan latarki da kamfanonin da suka siya NEPA wato Discos suka bukata a daukacin fadin kasar nan.

Bayanin karin farashin na hukumar yana kunshe ne a cikin rahoton data fitar mai taken, ‘Duba farashin wutan lantarki tsakanin 2016-2018’ ga kamfanonin wuta.

Rahoton ya ci gaba da cewa, an fara aiwatar da sabon kari farashin ne tun a ranar daya ga watan Yulin, ahekarar 2019.

Kamfanonin sun sun kuma sanar da cewa, an yi sabon karin farashin ne saboda rashin cin riba a bangarensu wanda ke hanasu cigaba da zuba kudi cikin kasuwancin.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2018, kamfanonin sunyi ikirarin cewa sun tabka mumnunar asarar a yayin da suke sayan wutar lantarki a kan naira 80.88, inda su kuma suke sayar da wutar a kan a farashin naira 31.50, inda hakan ke nuna cewa, sun yi asarar naira 49.38 ga kowani kilon wuta.

A cewar rahoton,manufar karin sabon farashin na wutar lantarkin, shine sauyi cikin abinda amfani daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2018 domin sanin irin riba da yin asara.

Exit mobile version