Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

An Kara Samun Kudin Shiga Ta Hanyar Kiwon Kaguwa A Kunshan

Published

on

Duk da yanayin fuskantar cutar COVID-19 a bana, mai kiwon kaguwa a garin Bacheng na birnin Kunshan dake lardin Jiangsu, Chang Jianhua bai damu da sayar da kaguwa ba, domin akwai dandalin aikin noma mai amfani da fasahohin zamani a wurin. Tun kaddamar da dandalin a shekarar 2018, an riga an kafa ma’aunoni 2000 bisa fannoni 186. A halin yanzu, masu kiwon dabbobi suna iya sa ido ga kididdigar yanayin ruwa kai tsaye ta dandalin.

A birnin Kunshan, an samarwa mutane dubu 40 zuwa 70 ayyukan yi ta hanyar kiwon kaguwa, kuma yawan kudin shiga da aka samu daga sha’anin a kowace shekara ya kai fiye da RMB yuan biliyan 4.

Yao Kewei na kauyen Tianfu dake garin Huaqiao na birnin Kunshan, yana da burin fitar da tambarin kamfaninsa na samar da ’ya’yan itatuwa. A sakamakon kididdigar da aka gabatar bisa dandalin, yawan kudin shiga da ya samu a kowace shekara ya karu, daga dubu 250 zuwa dubu 400 a halin yanzu.

Ta hanyar dandalin, ana sa ran cewa, ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan kudin shiga na manoman wurin zai karu da RMB Yuan biliyan 2. Manoma wurin suna samun moriya daga fasahohin zamani, don haka suna hangen kyakkyawar makomar zaman rayuwarsu. (Mai Fassarawa: Zainab Zhang)
Advertisement

labarai