An Karrama Farfesa Salau A Jami’ar ABU

Malamai da tsoffin daliban tsangayar kimiyyar aikin jarida na jami’ar ABU da ke Zariya sun karrama Farfesa Salau Suleman a matsayin ‘Uba Mai Tausayawa’.

A cikin makon da ya gabata ne malamai da tsoffin daluban tsangayar kimiyar aikin jarida ta jami’ar Ahmadu Bello Zariya su ka karrama babban malami kuma farfesa a fannin aikin jarida bisa gudummawar da ya ba su a kan koyan aikin jarida a matsayin Uba Mai Tausayawa.

Taron an shirya shi ne a bubban dakin taro da ke sashen kasuwancia harabar jami’ar.

Wakilinmu na daya daga cikin manema labaran da su ka shaida da yadda taron ya gudana kuma ya aiko ma na da tsarabarsa.

Taron dai an shirya shi ne musamman don nuna irin gudummawar da kasurgumin malamin ya baiwa malamai da daliban da su ka tare da shi a da da kuma yanzu.

Hakan ya sa malaman da tsoffin daliban su ka tara makudan kudi don nuna godiyarsu gare shi tare da nuna mashi cewa su na tare da shi kuma ba su manta da kokarin da ya yi masu a rayuwarsu ba.

Hakan ya sa  taron  ya samu karbuwa ta bangaren malaman da su ka yi taraiya da farfesan a baya da yanzu daga bangaren cikin gida da wajen.

Farfesa Shola Adeyanjo ne ya fara yin bayanin makasudin taron inda ya ce, “a wannan rana a matsayinsu na malamai da su ke tare da Farfesa Salau Suleman da ke cibiyar kimiyar aikin jarida ta jami’ar Ahmadu Bello Zariya da kuma tsoffin daluban da Allah ya yi masu kumbar susa a halin yanzu mu ke so mu  karrama Farfesa Salau tare da kaddamar da wata littafi da ya shafi aikin jarida a kasarmu Nijeriya wanda su ka rubuta a tsangayar a matsayin karamci a gare shi bisa hidimar da ya yi wa al’umma a lokutan baya da yanzu.”

Bayan haka kuma Alhaji Ahmed Maiyaki, tsohon darakta mai kuda da hultar yada labarai a gwamnatin PDP ta jihar Kaduna karkashin tsohon gwamna, Lamaran Yero, ya gabatar da bayani a matsayinsa na shugaban tsoffin daluban da su ka shiryawa taron liyafar kasaita a matsayin  tasu gudunmawar don karrama Farfesan bisa kokari da taimakon da ya yi masu a lokacin su na dalibai.

Kuma ya ce, abin ban sha’awa shi ne bisa irin kyakywan halaiyan Farfesa Salau  ga malamai da dalubai sun nemi taimako kudi da zasu gudanar da hidimar na wani addadi amma kafin a zo wajan taro an sami taimakon da ya zarce abin da suke nema sau Uku yace, hakan ya nuna duk wanda yayi alkairi tabbas zaiga alkairi a rayuwarsa inji shi

Bayan haka ne aka bar manyan bakin da suka halacci taron da kowa ya furta albarkacin bakinsa game da Farfesan da aka taru dominsa wato Farfesa Salau Suleman.

Farfesa Ladi wacce ta zama Farfesa ta Farko mace a Arewacin Nigeria a fannin kimiyar aikin jarida wato Mass Communication itama cewa tayi. “ Wallahi samun kamar Farfesa Salau a yanzu sai an shirya hakuri da sanin ya kamata tayi fatan Allah yayi masa taimako kamar yadda ya taimakesu”

Shugaban NTA TB College shima ya nuni da Farfesa Salau a matsayin abin koyi ga al’ummar duniya baki daya yayi fatan Allah ya karawa Farfesan tsawon kwana don cigaba da morar albarkar dake tare dashi.

Bayan an kammala taron ne Wakilinmu mu ya sami zantawa da wanda aka taru dominsa wato Farfesa Salau Suleman akan karramawar da akai masa a wannan rana ko me zai ce?

Farfesa Salau yace,” Ina godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya sanyawa rayuwata Albarka har gashi wasu suna karramani akan halayena  don haka ina godiya Allah,kuma ina mika godiya ga malamai da daluban da suka shirya taron Allah yasaka masu da Alkairi  dukkan mutanen da suka sami damar zuwa don nunamin kauna ina masu godiya Allah ya biya masu bukatunsu na alkari duniya da lahira “

Koda Wakilinmu ya tambayi Farfesa Salau, ko me yasa ya zama mai sauki ga al’umma da har takai ga ake yabonsa  haka?

Sai Farfesan ya kada baki yace,shi yasan Allah mai tausayine kuma ya umurci bayinsa su zama masu tausayawa junansu wannan shine dalilin da yasa rayuwa ta zama a cikin tausayi kuma nima ina son a Allah ya taisayamin

Don Haka ina rokon Allah yasa mu zama masu tausayin junan mu.

Daga cikin manyan bakin da suka hallaci wannan taron sun hada da Sanata Sadik daga Jihar Nigar akwai shuwabanin tsangayar kimiyar aikin jarida daga jami’ar Bayaro ta kano da kaduna da sauran jami’o’i

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

Exit mobile version