A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wa masu bukata ta musamman taro dangane da girmama su da karrama wasu fitattin mutane da su ke bayar da gudunmawa ga wadannan bayin Allah.
Kadan daga cikin masu bayar da gudunmawar akwai Ballo isa Bayaro da Alhaji Sule Lamido, tsahon gwamnan Jihar Jigawa, sai shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishak da Alhaji Garba Baban Ladi, sai Kawu Idiris Hausawa da Hajiya Sadiya Adamu.
An yi wannan taro ne a dakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano.
Alhaji Bello Isa Bayero ya yi kira ga ’yan siyasa da masu mulki da masu hannu da shuni da su dinga taimaka wa wadan nan bayin Allah masu bukata ta musamman, domin su ma mutane ne kamar kowanne mutum, amma wasu abubuwan ba za su iya ba sai an taimaka mu su.
Tasiu Shehu Garko shi ne babban mataimaki ga gwamnan jihar Kano, inda ya isar da sakon gwamnati a wannan taro kan tattalin arzikin masu bukata ta musamman sakamakon Korona
Ya ce, kiran gwamnati shi ne, masu bukata ta musamman su garzayo su amfana da ilimi kyauta tun daga firamare har jami’a.
“Kuma zuwana wannan guri mai girma gwamna bai bari na zo haka kawai ba. Ya bada kayan abinci a ba su, kuma batun da gwamna ya yi na ilimin mai bukata ta musamman kyauta ne, ba shi kadai ba, a’a, hard a dansa, kuma duk matakan da za a kawo yaro mun dauki wannan.”
Shi ma Injiniya Musa Muhammad Shaga, shugaban gamayyar kungiyoyi masu bukata ta musamman ya bayyana watsi da a ke yi da su, ya ce, wannan ba shi da abinda ya fi damun sa kamar sa.
Ya ce, akwai yaransu da da dama da su ka gama karatu, amma maganar aiki babu. Amma ya ce, maganar karatu kyauta ne wannan babu matsala tun daga locacin Malam Ibrahim Shekarau ya zuwa yanzu babu abinda ya tsaya, amma maganar aiki shi ne akwai matsala.
“Da a na daukar aiki, to duk wannan surutun bara da an daina,” in ji shi.