Adamu Yusuf Indabo">

An Karrama Marubuciya Umma Sulaiman Saboda Ayyukan Jinkai

Jajirtacciyar ‘yar gwagwarmayar kare mata da kananun yara kuma shugabar gidauniyar tallafa wa mata da kananan yara da marayu da kuma masu bukata ta musamman, Women Children Dream Foundation, wato Hajiya Umma Sulaiman Shua’aibu ‘Yan Awaki, wacce aka fi sani da Aunty Baby, ta samu kambun karramawa saboda tarin hidimarta ga al’umma na ayyukan jinkai, wadanda suka karade birni da kauye.

Kamfanin Arewa Entertainment And Media Concept dake Zariya shi ne ya karrama Aunty Baby da kambun karramawa, saboda yabawa da irin gudunmawar da take ba wa al’umma da aikin jin kai da take yi a kullum ba dare ba rana.
A cewar shugaban kamfanin na Arewa Entertainment And Media Concept Zaria, Alhassan Abubakar Sadik cewa ya yi: “Da ma Arewa Entertainment And Media Concept ta saba karrama hazikan mutane da suke bayar da gudummawa a cikin al’umma a kowacce shekara. Don ko a bara ma mun karrama mutane Takwas ne. Amma a bana mun zabi mutane Uku ne kacal da za mu karrama. Kuma mun zabi Hajiya Umma ne a cikin wadanda za mu karrama ne saboda ayyukan ta na jin kai ga al’umma.”
Malam Alhassan Abubakar Sadik ya ci gaba da cewa: “A wannan bangare na jin kai da muka so karrama ta, an gabatar mana da sunayen mutane da dama, amma da muka yi bincike a kan dukkan wadanda sunayensu ya zo gabanmu, sai muka ga cewar Hajiya Umma Sulaiman ita ce wacce ta fi sauran cancanta da wannan karramawa. Saboda irin ayyukan ta da muka gani karara da idanuwanmu, bayan mun bibiyi shafukanta na sada zumunta a yanar gizo. A nan muka ga irin tarin ayyukan da take yi. Kama daga kan rubuce-rubucenta don wayar da kan al’umma musamman mata, da ba su shawarwari don inganta zamantakewar aurensu da kuma kula da lafiyar jikinsu, da kuma ba wa mabukata jari don su tsaya da kafafunsu, da daukar nauyin auren zawarawa da yi musu kayan daki, da kuma daukar nauyin karatun marayu. Don haka da wannan kowa zai yarda mun ba Hajiya Umma wannan kambun karramawa ne bisa cancanta, saboda mu mara mata baya da kuma ba ta kwarin gwiwa a kan irin ayyukan alherin da take yi ba tare da ta gajiya ba.”
Kamfanin dai na Arewa Entertainment And Media Concept Zaria, ya yi tattaki ne daga garin na Zaria har zuwa Kano domin karrama Hajiya Umma Sulaiman Aunty Baby a ranar Lahadi 24 ga Janairu, 2021, sakamakon dokar hana yin taruka da aka sanya a can Jihar Kaduna, saboda kauce wa kamuwa da cutar nan ta Korona dake saurin yaduwa a tsakanin al’umma.
Wannan ne ya sanya kamfanin ya yanke shawarar bin wadanda zai karrama din a bana har ofisoshinsu, domin abu ne dai da kamfanin ya saba yi duk shekara kuma ba ya fatan ya kuskure hakan a wannan shekara.
Don haka an bayar da wannan kambun ne a ofishin gidauniyar ta ‘Women Children Dream Foundation’ dake kan titin Gwarzo Road daura da sakatariyar NYSC No C4 Khairat Plaza.
Taron dai ya samu halartar kafatanin membobin gidauniyar ta WCDF irin su Com. Auwalu Garba danbarno, Sheikh Mustapah Jafar, Hajiya Badi’a Nuhu, Nasir Sulaiman, Adamu Yusuf Indabo da kuma Ayuba Muhammad danzaki. Kuma taron ya samu tagomashin halartar dan jarida Malam Mukhtar Yakubu Kano, Abdullahi Lawan Kangala, Salim Aminci, Khadija Rabi’u Indabawa da dai sauran su.

A cikin jawabin Hajiya Umma Sulaiman na godiya, bayan ta karbi kambun girmamawa daga hannun shugaban kamfanin na Arewa Entertainment And Media Concept Zaria Alhassan Abubakar Sadik, Hajiya Umma Sulaiman ta nuna farin cikinta da wannan karramawa da ta yi mata bazata saboda tana ga kamar ba ta yi komai ba, ashe kuma duniya  ta ga abun da ta yi har ma ta ci a yaba mata da kuma girmama ta.
Don haka ta godewa Allah da Shi ne ya zabo ta a cikin al’umma ba don ta fi kowa ba, Ya kuma sallada wadannan bayi naSa da su karrama ta. Kuma ta roki Ubangiji da kada Ya gajiyar da ita a kan ayyukanta na jin kai tare da yin tawassali da manzon tsira. Sannan ta godewa wannan kamfani da tawagarsa da suka yo tattaki tun daga Zaria har zuwa Kano don su karrama ta, tare da yi musu fatan komawa gida lafiya. Sannan ta yi kira ga jama’a da su zama masu taimako ga mabukata da kuma kyautayi da tausayin juna.
A lokacin da take tattaunawa da manema labarai kuwa, Hajiya Umma ta bayyana musu abun da ya ja hankalinta har ta tsinduma wannan aikin na jin kai da cewa: “Ganin yanayin rayuwa yanda al’amura suke tafiya, saboda dama yanayin rubuce-rubucena ya sa ina mu’amala da mata da yawa da kuka counseling and consultation don ba da shawarwari ga ma’aurata da kuma matsaloli kan zamantakewarsu da lafiyarsu da muke yi.
“Hakan ya sa na saba da mata. To ta nan ne na fahimci yadda rayuwar al’umma ta koma baren mata da kananun yara. Saboda mace ce za ta zo ma ga ta da yara kanana, miji ya mutu an bar ta da marayu, ko kuma ya sake da sauransu. To irin wannan ne na ga abun ya yi yawa, saboda tun ina iya taimaka da aljihuna, sai kuma abun yake nema ya fi karfina, domin waccan ta zo ta ce ga matsalarta, wannan ta zo ta ce ga halin da take ciki. To da dai na ga abun da yawa ba zan iya ni kadai ba, wannan dalilin ya sa na ce bari na bude foundation mu yi mata rijista yadda jama’a za su zo mu tafi tare cikin wannan hidima ta taimakawa al’umma.”
To, Hajiya Umma muna rokon Allah Ya dafa miki, ke da dukkan masu taimaka miki da sauran masu aikin jin kai Ya yi muku tukuici da Jannatul Ma’awa, amin.

Exit mobile version