An Karrama Marubuciyar Littafin ‘Amon Yanci’ A Katsina

A kokarinta na dabbakawa da daga darajar harkar adabi a kasa, musamman ma a jihar Katsina, kungiyar Marubuta Ta Kasa Reshen Jihar Katsina (ANAKATS) a ranar 7 ga Yuni, 2019 ta karrama marubuciyar littafin Amon ’Yanci, Malama Halima Ahmad Matazu, wanda kamfanin Gidan Dabino Publishers su ka wallafa a shekarar 2013 a wannan rana ta Lahadi a babban dakin taro na Pleasant Library and Book Club (Gidan Abba Saude) da ke kan hanyar Modoji a Katsina a yayin taron kungiyar na wata-wata (Monthly Reading Session).

Marubuciyar littafin, Malama Halima Ahmad Matazu, wadda mata ce ga shahararren marubuci kuma malami a harkar adabi a jami’ar jihar Kaduna, Prof. Ibrahim Malumfashi ta rubuta; kuma hau tauraron watan 7 (Guest writer).

Taron wanda a ka gabatar a wajen karfe wajen Karfe 4:00pm na ranar, ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen jihar da sauran marubuta da dalibar daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Katsina. Cikin manyan mutanen akwai Tsohon shugaban kungiyar marubuta ta jiha, Alh. Muhammad Kabir Sani, Malam Bishir Mamman mataimakin sakataren kungiyar kuma malami a College of Legal and General Students Daura, Dr. Abdu Sani Fari, Dr. Shamsudden Bello, Bello Hamisu Idda, Abdurrahman Aliyu, Lawal U.S Kangiwa, Malam Danjuma Katsina, Haj. Fatima Muhammad, Haj. Fadila Isyaku, Dr. Bashir Abu Sabe da Hajiya Maryam Kabir Mashi da sauransu.

A jawabin bude taro, shuguban kungiyar na jiha, Dr. Bashir Abu Sabe, ya fara da godiya ga Allah madaukakin sarki wanda ya bada ikon amsa gayyatar kungiyar da mahalarta taron su ka yi, sannan ya bada takaitaccen ayyuka da shuwagabannin kungiyar su ka yi daga sadda su ka amshi ragamar kungiyar daga tsofaffin shugabanni. Da kuma jeranta mutanen/marubutan da a ka yi irin wannan taro a kansu. Ya lissafta su kamar haka:

– Rtd. Commissioner of police, Alh. Mudi  Kurfi

– Alh. Ummaru Danjuma Kasagi (Kulba na barna)

– Mal. Nasir (Wakokin zube) Umaru Musa Yar’adu Unibersity

– Haj. Halima Ahmad Matazu (Amon Yanci)

Shugaban kungiyar yace makasudin gabatar da wannan taro shine a ba marubuci dama ya baje fasaharsa akan littafinsa walau an buga ko ba’a buga ba, sannan mahalartan taron su yi ma sa tambayoyi yana amsawa. Sannan ya fadi dalilai na rubutashi, tasirinsa ga al’umma.

Daga karshen jawabin ya kira marubuta a ciki da wajen jihar su taimaka wajen ganin dorewar wannan yunkuri na kungiyar.

A lokacin da a ka kira marubuciyar domin ta fede biri har witsiya akan littafin nata, ta fara ne da bada takaitaccen tarihinta inda tace an haifeta ne a garin Maatazu, ta karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina. Tayi karatun Firamare, Sakandire da Jami’a inda ta yi digiri na daya dana biyu. Tana da aure da Ya’ya da Prof. Ibrahim Malumfashi.

A yayin da take gabatar da littafin nata, ta fara ne da bayyanacewa sha’awar karance-karance ne tun tana aji ukku a Jami’a yasa ta fara rubuta wannan littafi wanda tace itace tata gudunmawar ga fafutukar da gwagwarmaya da akeyi wajen ganin mata sun samu ‘yancin su, amma ba irin ‘yancin da ake yaudarar mata akai ba.

Littafin ‘Amon Yanci’ yana bada labarin wata yarinya ce mai sune Mairo wadda ta shiga kunci, musgunawa, har da kokarin yi mata fyade da rashin kyautatawa; amma bayan nan ta cimma nasara a rayuwarta tare da taimakon wata Lauya (Lawyer) mai suna Pamela wadda ta tallafi ita Mairon a rayuwa har itama ta zama Lauya.

A cewarta, labarin nata ya na faruwa zahiri a rayuwa. Ta cigaba da cewa babban sakon littafin nata shi ne jawo hankulan al’umma, a kan tauye hakkin yara mata a cikin al’umma. Ta cigaba da cewa ‘yanci kam ba ya samuwa sai dai a lahira, amma idan an bi koyarwa ta addinin Musulunci, to za a zauna lafiya, saboda Musulunci ba abinda ya rage ma ’yan adam na tsarin rayuwa. Bin dokokin Allah shi ne kadai mafita ga wannan al’umma.

Exit mobile version