An Karrama Ministar Jinkai Da Kyauta Mafi Daraja Kan Aikin Agajin Korona

Agajin

Daga Nasir S. Gwangwazo

 

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta karbi wata babbar karramawa ta duniya kan rawar da ta taka wajen aikin agaji lokacin da annobar korona (Cobid-19) ta barke a Nijeriya a farkon wannan shekara.

An karrama ministar ne da kyautar da a ke kira ‘EuroKnowledge Leadership and Humanitarian Award’ saboda babbar gudunmawar da ta bayar ga jama’a a daidai lokacin da annobar ta yi kamari a kasar nan.

Kamfanin EuroKnowledge, wanda ya shirya bikin karramawar ta hanyar yanar gizo daga Majalisar Dattawan kasar Birtaniya (House of Lords) a ranar Juma’a, ya bayyana jin dadi tare da yabo ga wasu shugabanni da su ka nuna kyakkyawan misali ta hanyar bada muhimman gudunmawa mai tasiri a sassan rayuwa da su ke aiki a ciki.

A jawabin ta na karbar kyautar, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta gode wa kamfanin  Euro-Knowledge, wanda ya na daga cikin nanyan kamfanoni masu bada shawara a duniya, saboda dacewar da ya ga ta yi da wannan karramawa. Ta ce wannan ya zama shaida na kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tunkara tare da magance matsalolin da cutar korona ta haifar ga ‘yan Nijeriya.

Ta ce: “Ina so in bayyana godiya ta ga EuroKnowledge saboda zaba ta da su ka yi, su ka ba ni wannan kyauta mai suna ‘Best National Humanitarian Response to COBID-19 Crisis Award’ a Majalisar Dattawa da ke London. Na gode da ku ka lura da aikin da mu ke yi wa al’umma.”

Ministar ta ce aikin da a ke yi yanzu na agajin jama’a, farawa ne ma na abin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shirya a burin ta na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin fatara da yunwa nan da shekara goma masu zuwa.

Ta ce, “Wannan karramawa ba wai tawa ce ni kadai ba, a’a, har ma da Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi da ma mutane da hukumomi da ke Nijeriya wadanda ke aiki tukuru domin su agaji milyoyin ‘yan Nijeriya wadanda annobar korona ta shafi samun kudin su.

“Ina so in bayyana sadaukarwar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ne ya kafa Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa. Aikin wannan ma’aikata shi ne samar da nagartacciyar hanyar da za a gudanar da ayyukan jinkai na kasa da na duniya don tabbatar da cewa an rage tare da shirya wa faruwar bala’i, da gudanar da  ayyukan taimakon jama’a a Nijeriya. Kuma na sadaukar da wannan karramawa ga abokan aiki na.”

Hajiya Sadiya ta ce wannan karramawa ta ba ta kwarin gwiwa domin ta kara kaimi bakin iyawar ta wajen yi wa ‘yan Nijeriya aiki.

Wasu wadanda su ma an ba su irin wannan kyautar karramawar sun hada da Sallo Polak (Babban Darakta na Philanthropy Connections a kasar Thailand), da Mai Girma Ernest Koroma (tsohon Shugaban Kasar Saliyo), da Mista Christian Paradis (tsohon Ministan Ciniki da Masana’antu na kasar Kanada), da Benedict Lee (sabon shugaban Kulob din Rotary a kasar Hong Kong), da Mista Tsbi Gal (tsohon shugaban bankin Morgan Stanley da ke Amurka), da Dakta Manu Chandaria (wani biloniya a kasar Kenya kuma shugaban kamfanonin Comcraft Group, Kenya)

Wasu ‘yan Nijeriya da su ma a ka karrama su sun hada da Dakta Mahmood Ahmadu (Shugaban kamfanin Integrated Online Services), da Miss Florence Otedola (shugabar cibiyar DJ CUPPY Foundation), da kuma Dakta Anthony Nwachukwu (shugaban kamfanin Innovate Pay 1).

 

Exit mobile version