An Karrama ‘Yan Wasan Nijeriya ‘Yan Ajin Shekara Ta 1994

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Nijeriya, kuma tsohon mai horar da tawagar Sunday Oliseh, ya yabawa hukumar kula da kwallon kafa ta kasar NFF, bisa girmama tsofaffin ‘yan wasan tawagar ta Super Eagles da suka wakilci Najeriya a shekarar 1994, yayin gasar cin kofin duniya da Amurka ta karbi bakunci.
Oliseh ya bayyana haka ne yayin bikin bada kyautuka da hukumar NFF ta gudanar a Otal din Eko da ke jihar Legas a daren ranar Litinin.
Sunday Oliseh ya ce tsofaffin ‘yan wasan tawagar na Super Eagles sun fi damuwa da karrama sunayensu kan gudunmawar da suka baiwa Najeriya, fiye da basu kyautar kudade, inda ya bada misalin yadda gwamnatin jihar Delta ta sanyawa babban filin wasanta da ke garin Asaba sunan Stephen Keshi, tsohon dan wasan Najeriya kuma tsohon kocin tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles.
Yayin bikin bada kyautukan da karrama ‘yan wasa, masu horarwa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kwallon kafar ta Najeriya, dan wasan gaba na Super Eagles, Ahmed Musa ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kasar na bana.
A bangaren tawagar kwallon kafa ta mata kuwa, Onome Ebi ce ta zama zakara tsakanin takwarorinta na Super Falcons, inda ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan Najeriya ajin mata wadda ake bayarwa duk shekara.
Tawagar kwallon kafar Najeriya ajin mata ta Super Falcons ce ta lashe kyautar tawaga mafi kwazo, yayinda magoya bayan Kano Pillars suka lashe kyautar magoya baya da suka fi da’a da nuna kwarewa wajen nuna goyon baya a kakar wasa ta shekarar 2018 da 2019.

Exit mobile version