Daga Rabiu Ali Indabawa,
Wata Kotu da ke zamanta a Ibadan, ranar Laraba, ta raba auren da aka shafe shekare 15 tsakanin wani makanike, Adeyemi Bamigbola da matarsa, Bidemi, kan zargin rashin aminci. Da yake yanke hukunci, Cif Henry Agbaje, Alkalin, kotun ya ce ya warware alakar da ke tsakanin Bidemi da Bamigbola ne domin a samu zaman lafiya.
Agbaje ya ba Bidemi rikon yaran biyu sannan ya umarci Bamigbola da ya biya Naira 10,000 a matsayin kudin alawus na kula da yaran a kowane wata. Tun da farko, Bamigbola ya garzaya kotu yana neman a raba auren bisa hujjar cewa matarsa mazinaciya ce da ba ta tuba ba. ”Yan sanda sun taba kama ta a Oyo tare da kwarton nata, wanda aka fi sani da Jomo.
Bidemi, wata ‘yar kasuwa ta zargi mijinta da rashin rikon amana. “Bamigbola ba ya son kula da ‘ya’yanmu biyu da kuma ni. “ Lokacin da mai gidan da muke a gidansa ya yi yunkurin korarmu saboda rashin biyan kudin hayar gida, sai na samu rancen kudi don biyan bashin. “Mafi munin har yanzu, Bamigbola mashayi ne kuma wanda bai son kula matarsa. “Yana kawo mata har gida ya rika kwanciya da su a gadonmu na aure, kuma yana yawan yin amai a daki duk lokacin da ya dawo gida a buge,” in ji Bidemi. NAN