An Kashe Babban Dogarin Sarkin Saudiyya

‘Yan Sanda a Saudiyya sun bayyana cewa an kashe babban dogarin Sarki Salman a daren Asabar bayan dogarin ya samu rashin jituwa da daya daga cikin abokansa. An kashe Manjo Janar Abdel Aziz al-Fagham ya yin wata ziyara da ya kai a gidan abokinsa da ke Jiddah, tafiya mai nisa daga arewacin fadar da Sarkin yake hutu a lokacin bazara.

Bbc Hausa sun labarto cewa; ‘yan sanda sun bayyana cewa an samu rashin jituwa tsakanin dogarin da kuma wani abokin nasa na daban mai suna Mamdouh bin Meshaal Al Ali da shi ma ya kai ziyara gidan da dogarin ya je.

Sun ce ana cikin wannan gardama abokin ya fita daga daki ya dauko bindiga sannan ya bude wuta ga dogarin Sarkin. Sai dai wanda ya yi harbin ya ki mika kansa ga ‘yan sandan da suka zagaye gidan bayan lamarin ya faru, wanda hakan ya jawo aka kashe shi har lahira.

Jami’an tsaro kusan biyar suka samu raunuka sakamakon musayar wutar da suka yi da abokin.

Bayan musayar wutar, an dauki Janar Fagham inda aka tafi da shi zuwa asibiti inda a can ne ya rasu.

Marigayin na da kusanci kwarai da Sarki Salman ganin cewa sun dade tare.

Sarki Salman ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015 a lokacin yana da shekaru 79.

Sai dai jama’a da dama na ganin dansa wato Yarima Mohammed bin Salman yana da karfin iko sosai a kasar.

Exit mobile version