An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa.
Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori.
- An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur
- Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi
Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani Ɗan banga na yankin ya mutu bayan da wani bam ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaron yankin.
A cewarsa, motar ‘yansandan da ke sintiri ta ofishin ‘yansanda na Garaha ita ma ta ƙone yayin da wani abun fashewa ya fashe acikin motar amma babu wani mutum da ya rasa ransa.
Shugaban ya ce, tsoron bama-baman da maharan ke amfani da su ya sanya zuwa wuraren da aka kai hare-haren ke da matukar wuya.
Wa’aganda ya buƙaci a tura sojoji yankin da kuma tallafa wa waɗanda harin ya rutsa da su.