Daga Sulaiman Ibrahim,
A kalla mutane 18 ne aka kashe wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wani sabon hari da aka kai a kauyen Ancha dake gundumar Miango a masarautar Irigwe a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Lamarin ya zo ne kwanaki 10 bayan kashe wasu mutane uku a kauyen Rafin Bauna da ke karamar hukumar Bassa.
Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’, rundunar tsaro da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba.
Gwamnan Jihar, Lalong ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Filato da Hukumar Samar da Zaman Lafiya da su bayar da agajin gaggawa.