Sabbin hare-haren da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai kan iyakokin jihohin Kano da Katsina sun yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane uku, sannan aka yi garkuwa da wasu a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa na jihar Kano.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa, maharan dauke da manyan makamai, wadanda ake kyautata zaton sun tsallako zuwa jihar ne daga makwabciyarta, jihar Katsina, sun fara kai hari a kauyen Yanganau da ke karamar hukumar Tsanyawa a ranar Alhamis da yamma, amma jami’an tsaro suka kore su bayan musayar wuta.
- Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
Wani mazaunin garin wanda ya tattauna da manema labarai kan lamarin ya ce, “‘Yan bindigar sun fito ne daga Kogari a karamar hukumar Musawa/Matazu ta jihar Katsina. An sanar da jami’an tsaro da misalin karfe 5:30 na yamma, kuma bayan musayar wuta, maharan sun tsere ba tare da sun yi sanadiyyar asarar rayuka ko satar dabbobi ba.”
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.














