An Kashe Mutum 57 Cikin Kwana 2 A Sokoto –Rahoto

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta turanci ta wallafa yau Alhamis ta bayyana cewa mutum 57 ne suka rasa ransu a hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan jihar Sokoto. Rahoton ya bayyana cewa adadin mutanen an kashe su ne tsakanin ranakun Lahadi da Litinin din da suka gabata, inda a garin Goronyo aka kashe mutum 43, sai mutum 14 a yankin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoton.

Mazauna yankunan Sabon Birni sun tabbatar da adadin wadanda aka kashe, inda suka ce maharan sun kashe mutum daya a Unguwar Lalle, mutum tara a kauyen Tsangerawa, sai mutum hudu a kauyen Tamindawa. Sannan sun bude wuta a kauyen Gajid inda suka kashe mutum 3 ciki harda matukin babur.

Hakan nan a karamar hukumar Illela kan iyalar Nijeriya da Nijar, ‘yan bindigar sun harbe mutum 13, da tsakar daren ranar Lahadi. Duk kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Kamaluddeen Okunlola ya ce a wajensu adadin wanda suka rasa ransu mutum takwas ne kawai, amma shaidun ganin da ido sun tabbatar da adadin ya fi haka.

Exit mobile version