An Kashe Mutum 888, An Yi Garkuwa Da 2,553 Cikin Wata 9 A Kaduna

el-Rufai

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa sama da mutane 888 aka kashe tare da yin garkuwa da 2,553 a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Satumba 2021.

Gwamnatin ta kuma kara da cewa mutane 720 suka sami rauni a cikin wannan lokacin sakamakon hare-haren ‘yan bindigar.

Da yake gabatar da rahoton tsaro na kwata na uku a Kaduna a jiya, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce an kashe ‘yan bindiga 220 yayin da aka sace shanu sama da 12,000 cikin watanni tara.

Aruwan ya ce an kashe mutane 325 a jihar a farkon kwata, 222 a kashi na biyu, yayin da aka kashe 343 a kashi na uku, jimillar 888.

Kwamishinan ya ce an yi garkuwa da mutane 949 a farkon kwata, 774 aka sace a kashi na biyu yayin da aka yi garkuwa da mutane 830 a cikin watanni ukun da suka gabata.

Exit mobile version