Yusuf Shuaibu" />

An Kashe Mutum Daya, An Yi Garkuwa Da Uku A Suleja

An bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun mamaye garin Suleja da ke cikin Jihar Neja, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu mutum uku. Lamarin ya faru ne a yankin Chaza da kuma shalkwatar jam’iyyar PDP a daren Asabar. Wasu mazauna yankin sun bayyana wa manema labarai a ranar Litinin cewa, ‘yan bindigan sun mamaye yankin Chaza ne da misalin karfe tara, inda suka samu rshin nasara wajen yin yunkuri da wani mutum a yankin. Mutumin da suka yi yunkurin yin garkuwa da shi ya gudu da bayan gidansa lokacin da suka isa cikin gidansa.

Shugaban ‘yan kungiyar sa-kai na yankin mai suna Dantani Jarumai ya bayyana wa manema labarai cewa, an harbe mutum biyu daga cikin mazauna yanki a wannan farmakin lokacin da suke zuwa wajen da labarin ya faru tare da sun sani ba. Ya kara da cewa, nan take daya daga cikin su ya mutu, yayin da dayan aka harbe shi a hannunsa, inda aka garzaya da shi zuwa babban asibitin garin Suleja.

Ya ce, tawarsa tare da hadin giwar sojoji da kuma ‘yan sanda suka bi sahun maharan bayan da suka ji karar bindiga, maharar sun gudu daga yankin. Shugaban ‘yan kungiyar sa-kai ya ci gaba da cewa, washagarin ranar ne ake samun labarin cewa, ‘yan bindigan sun kai hari a shalkwatar jam’iyyar PDP a makwabciyar yankin.

Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, a yankin na biyu ne ‘yan bindigan suka yi garkuwa da wani ma’aikacin gwamnati wanda yake aiki a garin Abuja, haka kuma sun yi garkuwa da wata mata tare da ditarta wanda mijinta ya gudu lokacin da maharar suka shiga gidansa.

Lokacin da wakilinmu ya tuntubi sabon shugaban ‘yan sanda na yankin Suleja, ACP Sani Badarawa, ya bukaci wakilinmu ya tuntunbi rundunar ‘yan sandar jihar da ke garin Minna domin jin karin bayani a kan lamarin.

 

Exit mobile version