An Kashe Mutum Fiye Da 3,000 Cikin Shekara Biyar A Zamfara –Gwamna Yari

Gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewa barayi sun kashe mutum kusan 3,526 a cikin shekaru biyar, gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yab Sandan Nijeriya, Muhammad Adamu ya ziyarci jihar.

‘Kusan kauyuka 500 aka share, an jiwa akalla mutum 8,219 raunuka, wasu daga cikin masu raunin har yanzu suna jinya.’ inji Sakataren gwamnatin jihar

‘’Tattalin arzikin jihar Zamfara ya nakasa sosai, an wawashe daruruwan shaguna, sannan mutanen masu yawan gaske sun rasa muhallin su, mutane masu daman gaske sun shiga halin kaka-ni-kayi, al’umma ko bacci basa iya yi.’ inji Sakataren

Yari ya bayyana cewa akwai rahoto da gwamnatin jihar ta tattara, mai shafi sama da 7,000, inda aka yi bayyani tsaf kan rikicin na Zamfara tun daga shigowar tsageru daga Libiya da kuma ‘Yan Boko Haram.

Exit mobile version