An Kashe Sama Da Mutum 20 A Zamfara

Daga Hussaini Baba Gusau

Tashin hankalin da ake tunanin yin bankwana da shi ya dawo a Jihar Zamfara, inda a jiya aka kashe sama da mutum 20 a kauyen Bawar Daji dake Karamar Hukumar Anka.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa LEADERSHIP A Yau cewa, a shekaran jiya ne Maharan suka yi wa al’ummar garin Bawar Daji kwantar bauna a lokacin da suke tattaunawa da ‘yan sa kai, domin bullo da hanyoyin da za su magance matsalar mahara kafin damina ta kankama.

Majiyar ta mu ta ci gaba da bayyana cewa; “Su na tsaka da wannan tattaunawa ne sai maharan suka kewaye su, inda suka fara ruwan harsasai kan mai uwa da wabi, a nan take suka kashe mutane goma.

“Washegari, a jiya kenan lokacin da ake shirin jana’izar wadannan mutane goma da maharan suka kashe, sai ga su sun sake bayyana, inda suka kashe sama da mutum 20 nan take.

“Sun ci gaba da aikata kisan mummuke, ta yadda duk wanda ya gudu sai su bi shi su harbe, mata da kananan yara wadanda ke cikin gidajensu ne kawai suka tsira.” inji majiyar

LEADERSHIP A Yau ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Shehu Muhammad ya bayyana mana cewa, rundunarsu ba ta da labarin abin da ke faruwa a Dansadau, amma a kauyen Bawar Daji dake Karamar Hukumar Anka su na da labarin an kashe mutane uku ba sama da Ashirin ba.

Exit mobile version