Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta shaida cewar wasu ‘yan daba sun farmaki caji ofis din ‘yan sanda da ke Umuoba da ke karamar hukumar Isiala Ngwa a jihar inda kuma suka hallaka jami’in dan sanda guda mai mukamin Insifekta.
Kakakin Rundunar, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a jiya tare da cewa ‘yan daban sun kai harin ne a ranar Litinin da misalin karfe 3:30am na ranar.
Ogbonna ya kuma ce harin da ‘yan daban suka kai ya janyo konewar caji ofis din da kuma motocin zirga-zirga na ‘yan sanda sakamakon sanya musu wuta da ‘yan daban suka yi.
“A sakamakon wannan harin, an yi rashin jami’in dan sanda mai mukamin Insifekta, da kuma wani dan sanda da ya gamu da munanan raunuka.
“Yan daban sun dire cikin ofishin ‘yan sandan inda suka balle wurin ajiyar makamai tare da sace wasu daga cikin makaman da aka ajiye ciki har da bindigan da suka yi amfani da shi wajen kashe Insifekta.
“Sun kuma banka wuta wa ofishin ‘yan sandan tare da kona motocin da suke fake a cikin harabar wurin.
“An dauki gawar dan sandan da aka kashe zuwa dakin adana gawarwaki shi kuma dayan dan sandan aka jinkata na amsar kulawar likitoci,” inji shi.
Ogbonna ya shaida cewar rundunar ‘yan sandan jihar Abia tunin ta kaddamar da bincike kan wannan lamarin domin gano wadanda ke da hannu a kai wannan harin domin hukunta su daidai da laifukansu.
Ya nemi jama’a da a kowani lokaci suke sanya ido wajen ganin sun sanar da hukumomin tsaro rahoton duk wani batagarin da basu yarda da shi ba domin daukan matakan da suka dace cikin gaggawa.
Ya kuma nemi jama’a su rika bin doka da oda a kowane lokaci tare da cewa aiki ne akansu su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.