Gundumar Huan ta birnin Qingyang dake lardin Gansu na kasar Sin, tana yankin kan tudun Liupan, yanki ne mai fama da kangin talauci, inda ake kiwon tumaki cikin tsawon lokaci a tarihi.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, mazauna gundumar sun sanya kokari, kan aikin kiwon tumaki domin kubutar da kansu daga kangin talauci.
Sun Zhixue, manomin kauyen Xigou na garin Quzi, mazaunin gundumar ne, wanda ke da shekarun haihuwa 43, ya taba fama da talauci mai tsanani, saboda matarsa ta kamu da cuta mai tsanani.
Ya zuwa shekarar 2013, ya samu rancen kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 50 daga gwamnati, daga nan ya fara kiwon tumaki, amma ya gamu da matsala, duk da haka bai bar sana’ar ba, daga baya a karkashin taimakon gwamnatin garinsa, ya samu riba a shekarar 2016. Ya zuwa shekarar 2019, adadin tumakin da ya yi kiwonsu sun riga sun kai sama da 300. Abu mai faranta rai shi ne, kudin da ya samu daga sana’ar ya kai yuan dubu 100.
Hakika a kauyen Xigou, kusan daukacin mazaunansa suna kiwon tumaki ne, darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Liu Xiaobing, ya yi bayani da cewa, a shekarar 2019, matsakaicin kudin shigar ko wanen manomin kauyen ya kai yuan 9,363. A fadin gundumar Huan kuwa, matsakaicin kudin shigar da aka samu daga sana’ar kiwon tumaki na ko wane manomi ya kai yuan 5000 a shekarar 2020.
To ina dalilin da ya sa sana’ar kiwon tumaki ta kawo manyan sauye-sauye a gundumar Huan?
Darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na gundumar Chai Chun ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2015, gaba daya gundumar ta zuba jarin da yawansa ya kai yuan sama da biliyan 1 da miliyan 100, a aikin kiwon tumaki, kuma kawo yanzu iyalai dubu 48 na gundumar suna kiwon tumaki, har ma yawan tumakin ya kai miliyan 2.1. A sa’i daya kuma, suna gudanar da ayyukan dake da nasaba da kiwon tumaki. Alal misali, yanka tumaki, da sarrafa naman tumakin, da kuma sayar da naman.