Nasir S Gwangwazo" />

An Kera Wa Jarumin Kannywood Sani Moda Sabuwar Kafa A Kano

An kammala kera wa fitaccen jarumin masana’antar shirin finafinan Hausa ta Kannywood, Sani Idris Kauru, wanda a ka fi sani da Moda, kafar katako, domin samun damar cigaba da tafiyar da rayuwarsa yadda ya kamata.
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne a ka yanke wa Jarumi Sani Moda kafarsa guda daya sakamakon fama da ya yi da ciwon sikari a asibitin Barau Dukko da ke Kaduna.
Bayan hakan ne sai jarumin ya yi balaguro zuwa makociyar jihar, wato Kano, inda a ka kera ma sa kafar da za ta maye gurbin waccan a asibitin kashi na gwamnatin tarayya da ke Gwauron Dutse a cikin birnin Kano.
A tattaunawarsa da wakillin LEADERSHIP A YAU, Malam Sani Moda ya gode wa Allah da abokan sana’arsa na Kannywood da kuma ’yan uwa da abokan arziki sannan da kuma musamman masoyansa bisa irin dimbin taimakon da su ka yi ma sa tare da ba shi kwarin gwiwa a tsawon lokacin da ya shafe ya na fama da wannan jinya. Ya kara da cewa, “an kammala aikin hada kafar a jiya (Litinin), sannan yau (Talata) an koya min yadda zan yi aiki da ita da kuma koyon tafiya.”
Daga nan sai ya tabbatar wa da LEADERSHIP A YAU cewa, zai koma Kaduna yau (Laraba), don cigaba da tafiyar da harkokin rayuwarsa na yau da kullum, kamar yadda ya saba.

Exit mobile version