Hussaini Yero" />

An Killace Daktan Da Ya Shigo Da Tsarabar Korona Zamfara Daga Malesiya

Kwamishinan Lafiya na Jihar Zamfara , Hon Yahaya Muhammad Kanoma ya bayyana cewa , yanzu haka suna killace da Daktan da ya dawo daga Malesiya Karatun Dakta da ke dauke da cutar Korona yana amsar magani a Asibirin Danba a nan Gusa.

Hon Yahaya Muhammad Kanoma ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke kaddamar da bita akan yadda za’a raba Gidan Sauro  , ga musu ruwa da tsaki akan kiwon lafiya da kungiyoyi masu bada tallafin akan kiwon lafiya da ‘Yan jaridu a dakin taron Ma’aikatar Lafiya da ke Sakatariyar Bala Yakubu da ke Gusau .

Hon Yahaya Kanoma ya kara da cewa , Babban mutum ne a Zamfara ya tafi kasar malesiya Karatu kuma ya kammala Karatunsa sai kashi yayo masu tsarabar cutar Korona ,kuma duk inda aka kai jininsa dan gwaji sun tabbatar mana yana da shi yanzu haka yanan a killace yana amasar magani inji Kwamishinan .

Kwamishinan ya bayyana cewa , Batun tallafin da Hukunar NCDC ko gwambatin tarayya, babu tallafin da gwamnatin jihar Zamfara ta samu daga garesu.

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ,  ta yi iyaka kokarinta wajan ganin an dakile wannan annobar Korona kuma duk kayan aikin da muke bukata a Asibitocin mu na gwaje gwajen cutar Korona gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya samar da su batare jiran tallafi daga hukumar NCDC ba ko gwamnatin tarayya.

Kuma yanzu babbar santar mu ta Danba ,babu Abu da ba asaba, kuma bama annobar cutar Korona ba  duk kan wasu annobar da ake tinanin zata iya samuwa munshirya yakarta da yardar Allah a wannan santa inji Kwamishinan .

Kwamishinan ya gode wa kafafen yada labarai da suka taimaka wajen jajurcewa akan fadakar da alumma wajen dakile annobar Korona a fadin jihar ta Zamfara.

Exit mobile version