Connect with us

Uncategorized

An Killace Matan Banza 18 Da Aka Cafke  

Published

on

Mata masu zaman kansau da kwastotminsu 18 ne jami’an ‘Yan Sanda suka cafke a wata liyafa da daddare a kusa da yankin Shasha da ke Akure, duk da dokar hana fita a Akure dake Jihar Ondo yayin aiwatar da dokar Korona.

Dukkanin wadan nan karuwai da masu yin shashanci da su an killace su a Akure, babban birnin jihar Ondo bisa zargin cewa sun kamu da cutar kwayar cutar Korona.

A cewar gwamnatin jihar, za su ci gaba da kasancewa a cibiyar killacewar har zuwa lokacin da sakamakon gwajin nasu zai fito na Korona.

An tattaro cewa an kama mutane 18 ne yayin gudanar wani aikin sa ido ne kan ayyukan hana zirga-zirga, domin abin da suke yi ya saba wa dokar gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita da hana yin taron jama’a.

Babban mataimaki na musamman ga gwamna kan ayyuka na musamman da dabaru, Dakta Doyin Odebowale wanda ya tabbatar da ci gaban lamarin, ya gargadi mazauna yankin da su yi biyayya ga dokar.

“An kama suna aiwatar da abin da bai dace a kuma haka ya saba wa  umarnin dokar hana fita. ” Mun kama su misalin karfe 10:30 na dare. Mun kawo su kungiyar likitocin don su zo su dauki samfuran jininsu domin gwaji. Har ila yau, an rufe gidan sayar da abinci. Za mu kira maigidan,” in ji shi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: