Rabiu Ali Indabawa" />

An Kone Tashar Jirgin Ruwan Nijeriya A Legas

Tashar Jirgin Ruwan Nijeriya

Wasu fusatattun mutane sun cinna wa Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), dake titin Marina, Legas wuta. Cikakkun bayanai game da yadda lamarin ya faru har yanzu ba a sani ba amma majiyoyi sun ce an banka wa ofishin wuta ne ta hanyar daukar fansa kan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya saboda tura sojoji a daren Talata don kai hari kan masu zanga-zangar a kofar Lekki, Legas.

Wata majiya ta ce masu kashe gobara a cikin gida daga NPA a halin yanzu suna gwagwarmaya don kashe wutar da ke ci. Mun yi kokarin jin ta bakin Shugaban na Hukumar NPA, Jatto Adams, amma abin ya ci tura saboda duk kiran da aka yi ba a amsawa, sannan kuma an tura sakonni ba amsa.

 

Exit mobile version