Umar A Hunkuyi" />

An Kori Manyan Jami’an ‘Yan Sanda 10, Takwas Sun Rasa Mukamansu

shugaban rundunar yan sanda

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kori wani babban jami’in ‘yan sanda mai mukamin Sufuritanda, da kuma masu mukamin mataimakin Sufuritanda su Biyar, gami da wasu manyan jami’an masu mukamin mataimakan Sufuritandan na ‘yan sanda su hudu daga aiki.

Haka nan kuma, hukumar ta amince da sauke wasu jami’an ‘yan sandan su Takwas daga kan mukaman nasu. Duk wadannan jami’an ‘yan sanda su 18 da abin ya shafa an yi masu hakan ne a sakamakon wasu laifuka mabambanta da su ka aikata na rashin da’a a aikin na su.
Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar a jiya, hukumar ta ce shawarar hakan ta taso ne daga wani taro na Takwas da hukumar ta yin a tsawon makwanni uku, wanda kuma ya kare a makon da ya gabata.
Sai dai hukumar ta ki ta ambata sunayen manyan jami’an ‘yan sandan da aka kora daga aikin kwata-kwata.
Sanarwar hukumar ta na cewa, “an sallami wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda (DCP) da kuma wasu masu mukamin babban Sufuritandan ‘yan sanda (CSP), da a ka sauke masu mukamansu, wanda hakan ya shafi masu mukamin Sufuritanda (SP) na ‘Yan sanda su hudu, da wani mataimakin Sufuritanda na ‘yan sanda (ASP) guda daya.
Hakanan hukumar ta amince da yin horo a kan wasu jami’an ‘yan sandan su 16, da kuma bayar da takardar gargadi ga wasu su hudu.
“Hukumar kuma ta na kan yin nazarin horon da aka bai wa wasu su 83, da su ka hada da wasu 18 da su ka daukaka kara.
“Hakanan hukumar ta kuma amince da yi wa wasu jami’an ‘yan sandan su 6,618 karin girma da su ka hada da wani guda mai mukamin AIG zuwa mukamin DIG, da kuma wasu guda Uku masu mukamin DCP zuwa mukamin CP, duk in ji sanarwar.

Exit mobile version