Wata tsohuwar sarauniyar kyau a kasar Romania ta rasa aikinta saboda tsabar kyawun da ta ke da shi. Claudia Aredelean mai shekaru 27 ta wallafa sanarwar cewa asibitin ya nada ta mukami a kwamitinsa a dandalin sada zumunta. Hakan ya yi sanadin mutane suka rika sukarta da cewa saboda kyanta aka nada ta, hakan kuma ya janyo asibitin ta umurce da ta yi murabus An umurci wannan tsohuwar sarauniyar kyau ta yi murabus daga aikinta a asibitin ne saboda ‘kyan ta ya yi yawa’ kamar yadda LIB ta ruwaito.
An nada Claudia Ardelean, mai shekaru 27 ta yi aiki a kwamitin asibitin Pneumophthisiology Clinical Hospital a kasar Romania duk da cewa ba za a rika biyanta albashi ba. Ardelean tana da digiri biyu a aikin lauya da nazarin al’adun turawa.
Bayan samun aikin, ta yi farin ciki har ta wallafa a kafar sada zumunta a ranar 8 ga watan Fabarairu.
Tsohuwar sarauniyar kyan ta wallafa hoton selfie da ta dauka a gaban ginin asibitin inda ta rubuta: “Ina godiya saboda gudunmawa da amintaka da na samu daga Cluj Nationtal Liberal Party!”. Sai dai bayan hakan, wasu suka fara sukar ta suna cewa ta samu aikin ne kawai saboda kyau da ta ke da shi. Newspaper Click ta ce sakamakon sukar da aka yi mata, an tilasta mata yin murabusa saboda tana da “kyau da yawa”.