Abubakar Abba" />

An Kwato Dala Biliyan Bakwai Daga Hannun Bankuna

Gwamnantin Tarayya ta kwato bashin Dala biliyan bakwai daga hannun wasu bankunan kasuwanci da ke Najeriya a karkashin shirin ta na musamman daga 2006 zuwa 2008.

Shugaban shirin Mista Okoi Obono-Obla ne ya sanar da hakan a a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja, inda yace, bakunan sun jima basu mayar da kudaden ba.

Obono-Obla ya ce kudin da aka baiwa bankunan bashi ba kayuta bane kuma dole ne a karbo su don maido ga asususn gwamnatin.

A cewarsa, “ a yanzu haka muna akan bincike akan kudaden da a ka karbo da wasu yan Najeriya suka yi gaba da su kuma daya daga cikinsu su ne wadannan dala biliyan bakwai da Babban Bankin kasa CBN ya bawa bankunan na kasuwanci bashi a 2006, 2007 da kuma 2008.”

Ya ci gaba da cewa, bayan shekaru sha uku ko sama da haka wadannan bankunan basu maidowa da gwamnatin tarayya bashin ba kuma da muka bukaci a maido da kudaden, sai bankunan sukace wai kyauta aka basu.

Ya kara da cewa, kudaden mallakar yan Najeriya ne a saboda haka baza su kasance a matsayin kyuta ba domin banunan na wasu masu zaman kansu ne, inda ya yi alkawarin cewar, a shirye suke su karbo sauran kudin don maido ga asusun gwamnatin tarayya.

Obono-Obla ya bayyana cewa, a shirye suke su kara karbo wasu manyan filaye mallakar hukumomin ma’aikatar noma da raya karkara, inda yace wasu yan kasa marasa kishi ne suka yi kutse a cikin filayen.

A cewar sa, “ ina son in baku tabbacin cewar, zamu karbo dukkan filayen da kuma tabbatar da an hukunta wadanda suke da hannu a ciuki.

Ya kara da cewa, “ muna kuma kan bincike akan karbo filaye da dama wadanda mallakar y hukumar tashshen jirgin ruwa ne na kasa dake garin Kalaba, Warri, Koko, Sapele da kuma jihar Legas.”

Ya bayyana cewa, “ zamu kuma karbo daga bankin tarayya na Mortgage da kuma daga sauran hukumomi mallakar gwamnatin tarayya dake fadin kasar nan.”

A karshe yace, ya yi kira gay an Najeriya su taimakawa shirin da sahihan bayanai da zasu taimaka don a karbo sauran kayan gwamnati da wasu marasa kishin kasa suka yi awon gaba da su.

Exit mobile version