Connect with us

LABARAI

An Lalata Haramtattun Makamai 5,870 A Zamfara

Published

on

Kwamitin Shugaban kasa kan lalata kanana da manyan haramtattun makamai ya lalata makamai 5,870 a Gusau ranar Litinin, wadanda gwamnatin Jihar ta Zamfara ta karbo su.

Gwamnatin ta Jihar Zamfara ta amso makaman ne daga hannun ‘yan ta’addan da suka tuba suka mika wuya ga kwamitin Jihar na wanzar da zaman lafiya da sasantawa da kuma ajiye makamai, wanda mataimakin gwamnan Jihar, Ibrahim Wakkala, ke shugabanta.

Bikin lalata makaman an yi shi ne a filin kasuwar duniya ta Gusau, wanda shugaban kwamitin na shugaban kasa, Emmanuel Imohe, ya jagoranta.

Lalata makaman ya sami halartar gwamnan Jihar ta Zamfara, Abdul’aziz Yari, Mataimakin sa, Ibrahim Wakkala, wakilai daga manyan kungiyoyin duniya, EU, ECOWAS da UNDP da sauran cibiyoyin tsaro da Sarakunan gargajiya.

A jawabin sa, Mista Imohe, cewa ya yi, an yi bikin ne domin lalata makamai 5,870 da kuma albarusai wadanda aka amsa daga kwamitin gwamnatin Zamfara kan kwance damara.

“Baya ga karbowa da lalata makaman, daya daga cikin manufar wannan kwamitin na shugaban kasa shi ne inganta rayuwar al’umman da suka sallama makaman na su.

“Zamfara ta na daya daga cikin Jihohi bakwai da aka zaba domin fara gudanar da shirin.

Mista Imohe, sai ya yaba wa gwamnatin ta Jihar Zamfara kan shirin ta na amsar makaman wanda har ya kai ga ta iya amso sama da kananan  makamai 5,000 da albarusai da kuma manyan makamai masu iya sarrafa kansu.

“Ina farin cikin kasantuwa da wannan babban hobbasan na gwamnatin Zamfara, ina kirga wannan a matsayin manyan nasarorin da wannan kwamitin ya samu, ina kara yi ma kwamitin na kwance damara wanda mataimakin gwamnan, Malam Ibrahim Wakkala godiya, da kuma dukkanin wadanda suka bayar da gudummawa wajen wannan gagarumar nasara da aka samu.

“Ku na sane da cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wannan kwamitin ne a watan Afrilu na shekarar 2013, da nufin magance matsalar karakainan haramtattun makamai manya da kanana.

“Muna kuma aiki ne tare da manyan kungiyoyi na duniya da nufin kwance damarar makamai a kan iyakokin kasarnan da kuma bayar da agaji ga tubabbabun ‘yan ta’adda,” in ji Imohe.

A na shi jawabin, Gwamna Yari, ya godewa gwamnatin tarayya kan kafa kwamitin na shugaban kasa da kuma kungiyoyin duniya kan kokarin su na wanzar da zaman lafiya a Jihar da ma kasa bakidaya.

Gwamna Yari ya ce, Jihar ta gamu da kashe-kashe masu yawa da kuma asarar dukiyoyi sabili da matsalar ta masu satan shanu da ta’addanci.

Ya ce, wadannan asarorin ne suka tilasta kafa kwamitin na wanzar da zaman lafiya, sasantawa da kwance damara, wanda gwamnatin Jihar ta kafa.

“Tun bayan kafa kwamitin ya sami nasarar karban haramtattun makamai sama da 5,000 da kuma karban tuba daga ‘yan ta’addan masu yawa a fadin Jihar.

“A yau muna bukin lalata haramtattun makaman, za mu ci gaba da bayar da dukkanin taimakon da ya kamata ga kwamitin na Shugaban kasa wajen kyautata al’amarin tsaro a Jiharmu da ma kasa bakidaya.

“Za mu bayar da sahihin jerin sunayen tubabbun da suka sallama makaman su ga gwamnatin tarayya domin a taimaka ma su da hanyar da za su inganta rayuwar su.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: