An Nada Farfesa Maimuna Matsayin Shugabar Jami’ar FUGA 

Daga Muhammad Maitela,

Hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gashuwa (FUGA), ta amince wajen nada Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar shugabar jami’ar, wadda ita ce ta uku a jerin shugabanin makarantar kuma mace ta farko da za ta jagoranci ragamar jani’ar.

Hukumar gudanarwar ta sanar da hakan da yammacin ranar Asabar, a takardar sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen kula tare da harkokin yada labarai a jami’ar, Mista Usar Ignatius.

Hajiya Maimuna wadda Farfesa ce a fannin ilimin kimiyyar hada magunguna (Chemistry) ta gaji shugaban jami’ar mai barin gado, Farfesa Andrew Haruna wanda zangon mulkinsa zai kammala a farkon watan Fabarairun 2021.

Bugu da kari, Waziri ta samu nasarar shugabancin kujerar jami’ar ne bayan da ta doke farfesoshi 47 wadanda su ka fafata a zaben wanda ya gudana ranar 16 ga watan Junairun 2021.

A sanarwar amincewar hukumar gudanarwar jami’ar, na sakamakon zamanta na biyar da yammacin ranar Asabar, wanda shugabanta Ibrahim Akuyam, ya sanar ya bayyana cewa farfesoshi 48 ne suka bayyana sha’awar kujerar shugabancin jami’ar, wanda daga bisani 25 ne suka yi saura, sannan zuwa matakin karshe kuma, mutum uku ne su ka rage wanda a karshe hukumar gudanarwar ta zabi Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar shugabar jami’ar.

A karshe, da yake taya sabuwar shugabar murna, shugaban hukumar gudanarwar ya bukace ta da rungumi daukwacin ma’aikatan jami’ar tare da aiki da kowane bangare don ci gaban jami’ar.

Hoto: Farfesa Maimuna Waziri tare da Farfesa Andrew Haruna.

Exit mobile version