An Nada Musa Gafai Mamban Cibiyar KATCCIMA A Jihar Katsina

KATCCIMA

Daga Sagir Abubukar,

A kokarinta na bunkasa matasan ‘yan kasuwa, a jihar Katsina, Cibiyar Masana’antu da Kasuwanci da hako ma’adanai da kuma aikin gona ta jihar Katsina, wato (KATCCIMA) ta nada Shahararren Matashin dan kasuwar Nan, na jihar Katsina, kuma Shugaban Gidauniyar (Gafai Charitable Foundation) Kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Sadarwa Na Gafai, Alhaji Musa Yusuf Gafai, a matsayin daya daga cikin Daraktoci hukumar Gudanarwa Cibiyar, na tsawon shekara biyu.

Bayanin hakan, na kunshe a cikin wata takardar nadin, da Shugaban Daraktocin Cibiyar, Farfesa Sani Abubakar Luggah ya sanyawa hannu a ranar litinin, aka damkawa Matashin dan kasuwar a helkwatar Ofishinsa, da ke kan titin IBB da ke cikin garin Katsina da daraktocin cibiya da suka wakilci Shugaban.

Takardar ta nuna cewa sakamakon nadin Musa Yusuf Gafai ya biyo bayan irin jajircewarsa a lokacin da ya ke gudanar da huldar kasuwanci da kuma yadda yake muamala da jama’a. Dalilin kenan da ya sa muka amince da yi ma wannan nadin. Muna fatan wannan nadi ya zamanto ka ba wannan cibiya guddumuwar irin baiwar da Allah ya baka domin kai ta mataki na gaba, da yardar Allah.

Daga karshe, Farfesa Sani Abubakar Luggah ya taya Alhaji Musa Yusuf Gafai murnan samun wannan matsayi da kuma yin addu’a samun dawammamen zaman lafiya a Nijeriya da jihar Katsina.

Da yake tattaunawa da manema labarai, bayan amsar takardar sabon mukami da aka ba shi, Alhaji Musa Yusuf Gafai, ya bayyana jin dadinsa bisa ga wannan nauyi da aka dora masa, ya ce zai yi bakin kokarin sa da gogewar da ya ke da ita, wajen ganin cibiyar ta bunkasa bisa ga da. Kuma wannan wani sabon kalubale ne, amma da yardar za mu yi bakin iyawarmu don ganin harkokin kasuwanci da Masana’antu da harkar hakar ma’adanai da noma da kiwo sun bunkasa a jihar Katsina. Haka zalika, ya jawo hankalin matasan jihar Katsina da su zamo masu dogaro da kansu da kuma rike sana’o’in hannu don bunkasar rayuwarsu.

Matashin dan kasuwar ya mika godiyarsa ta musamman ga hukumar gudanarwa Cibiyar, a karkashin jagorancin Farfesa Sani Abubakar Luggah da sauran daraktocin bisa yadda suka zabo ni, na zama daya daga cikinsu, bisa ga cancanta ta da suka gani kan wannan mukami da aka ba ni, kuma da yardar Allah ba zan watsa masu kasa a ido ba.

Alhaji Musa Yusuf Gafai, Matashi dan kasuwar kuma burinsa kullum yadda zai taimakawa masu karamin karfi na lungu da sakon jihar Katsina, shi ya sanya ya kafa wata Gidauniyar ta tallafawa al’umma masu karamin cikin abinda Allah ya hore ma shi. Yana daya daga cikin matasa da su ka tsayin daka wajen samarwa matasan jihar Katsina abun yi.

Exit mobile version