Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Nada Sabon Mai Tsaron Fadar Shugaban Nijeriya Biyo Bayan Harbe-harbe

Published

on

Biyo bayan harbe-harbe da a ka samu a kwanakin baya a Fadar Shugaban Nijeriya sakamakon wani rikicin cikin gida, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon Babban Mai Kula da Tsaron fadar a jiya Litinin. Wanda a ka nada din shi ne, Mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Aliyu Musa.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a wata sanarwa, wacce mai magana da yawun fadar, Malam Garba Shehu, ya raba wa manema labarai, ya na mai cewa, an yi wa DCP Musa canjin aiki ne daga Shiyya ta 5 ta rundunar ’yan sandan Nijeriya da ke Birnin Benin, inda sanarwarta kara da cewa, DCP Musa dan asalin Jihar Neja ne.

“An nada Musa ne biyo bayan sauyin wajen aiki da wanda ya gada, CP Abulkarim Dauda, ya samu,” in ji Garba Shehu.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne a ka bayar da rahotannin cewa, wani sabani ya barke a fadar lokacin da Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari, ta jagoranci tawagar masu tsaronta zuwa gidan Mai Taimaka Wa Shugaba Buhari na Musamman, Sabiu Yusuf, wanda a ka fi sani da Tunde, inda a ka yi zargin sun nemi su killace shi ta karfi da yaji bayan da ya dawo daga Jihar Legas, wacce a ke kallo a matsayin hedikwatar annobar cutar Korona a Nijeriya.

Bayanan sun nuna cewa, turjiyar da Tunde ya yi ce ta haifar da samun harbe-harbe a wajen, lamarin da ya yi matukar sabawa da dokar zamantakewa ta Fadar Shugaban Nijeriya.

Jim kadan bayan hakan ne, Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya, Mohammad Adamu, ya bayar da umarnin kamawa tare da tsare jami’an tsaron Uwargida Aisha, lamarin da bai yi ma a dadi ba, inda har ta fito kafafen sadarwa na zamani ta na gunagunin lallai ya sakar ma ta su, don gudun kada su fuskanci barazanar kamuwa da Korona a hannun ’yan sanda wajen tsarewa.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, sannan daga bisani dai a ka saki jami’an uwargidan tasa tare da mayar da su bakin aikinsu. Abu na bayan nan daga a ka ji kan batun shi ne, wannan sauyi da a ka yi wa Babban Mai Tsaron Fadar tare da nada sabo a jiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: