An Nada Sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara

Gobara

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da nadin Liman Ibrahim a matsayin babban kontirola na hukumar kashe gobara ta Nijeriya, yau Alhamis shugaban kasar ya amince da nadin.

A wata sanarwa da sakatare mai kula da hukumomin kashe gobara, gidan yari, da ta shige da fice, Alhassan Yakmut ya sanyawa hannu yau Alhamis a Abuja, sannan ya bayyana cewa nadin zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Maris.

An nada Ibrahim din ne bayan da tsohon shugaban hukumar Mista Joseph Anebi ya yi ritaya a watan Maris din da ya gabata, sabon shugaban zai rike mukamin na tsawon shekaru hudu.

Exit mobile version