An Nada Sabon Shugaban Hukumar NYSC

Pic.3. Director of Welfare, National Youth Service Corps (NYSC), Mrs Bose Okakwu (L) and Director-General of the NYSC, Brig.-Gen. Suleiman Kazaure during their visit to sensitize Corps members ahead of Ondo 2016 Governorship Election in Akure on Tuesday (22/11/16). 8523/22/11/2016/ Segun Giwa/BJO/NAN

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da sabbin nade-naden mukamai da ta yi ga wasu manyan hafsoshin sojin, a wani matakin yin garambawul da gyaran fuska da babban hafsan sojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya gudanar a rundunar.

Kakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana wadannan sabbin nade-nade, inda yace Buratai ya amince da dauke da Manjo Janar Sule Kazaure daga hukumar NYSC dake kula yan bautan kasa, inda ya sauya masa wajen aiki zuwa cibiyar bayanai ta rundunar.

Rahotanni sun bayyana cewa Buratai ya nada Birgediya Janar S Ibrahim a matsayin sabon shugaban hukumar NYSC, bayan ya daukeshi daga jami’ar rundunar sojin kasa dake Biu, jihar Borno.

Har ila yau, a cikin sanarwar an bayyana dauke Birgediya Janar CA Bossman daga cibiyar littafai ta rundunar zuwa mukamin daraktan sashin kula da makarantun sakadandarin Sojoji dake duk fadin Nijeriya, yayin da Birgediya Janar E Angaye ya zama sabon darakta mai kula da tsofaffin Sojoji. Bugu da kari an dauke Birgediya BA Tsoho daga shelkwatar rundunar Sojin kasa zuwa cibiyar koyar da harsuna na rundunar Sojin kasa a matsayin babban kwamanda, yayin da Birgediya Janar AA Goni ya maye gurbin daya bari a shelkwata.

Sanarwar bata tsaya nan ba sai da sanar da dauke Birgediya Janar FC Onyeari daga sashin sufuri a shelkwatar rundunar Sojin kasa zuwa matsayin mukaddashin darakta mai kula da ciye ciye da tande tande.

Daga karshe babban hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da nada Birgediya Janar SS Ibrahim a matsayin sabon jami’i mai kula da daukan dalibai da daukan ma’aikata na jami’ar sojin kasa dake Biu

 

Exit mobile version