Mai girma Sarkin Kofa, Alhaji Nasiru Adamu Kofa, ya nada Alhaji Yusuf Dauda Kofa sarauta a matsayin Turakin Kofa ta Jihar Kano a ranar Lahadin da ta gabata. Alhaji Yusuf Dauda Kofa, wanda shi ne shugaban kungiyar bangaren ‘yan kasuwa masu sayar da citta da Tafarnuwa a kasuwar Mile 12.
Kafin Alhaji Yusuf Dauda Kofa ya samu wannan sarauta dai ya taba rike mukamai da dama a kasuwar ciki har da wannan mukamin da yake rike da shi a halin yanzu.
Taron nadin sarautar wanda ya gudana a harabar fadar magirma sarkin Kofa ya samu halartar shugaban kasuwar mile12 Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam da tawagarsa ta shugabannin bangarorin kasuwar da sauran al’umma da suka fito daga sassa daban-daban na Kano, Kaduna, Legas, Jos da katsina baki daya.
Makada, mawaka da sauran abubuwan da suka gudana na ban shaawa a wajen taron. Babban bako a wurin taron shugaban kasuwar ta mile I2, Alhaji Shehu Usman Jibirin da sakataren kasuwar Alhaji Idiris Balarabe Legas da ma’aji Alhaji sa’idu Usaini sarina da shugaban ciyamomin kasuwar Alhaji Abdullahi Tukur Kura, da Abdulgiyasu Sani Rano, shugaba ‘yan kasuwar tumatiri, sauran sun hada da shugaban bangaren karas da kabeji Alhaji Bala Yaro hunkuyi, da iyayen kasuwar shugaban kungiyar dattawan kasuwar Alhaji isa Mohammed da Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki, da Alhaji Abdulwahab tsoho Babangida, da sauransu.
A cewarsa tun yana yaro karami yake tare da kyawawan dabiu masu kyau wadanda za su koya wa matasa na baya masu tasowa tarbiyyar tagari shi ma ana sa tsokacin shugaban kasuwar ta Mile I2 Alhaji Samfan ya nuna farin cikinsa a game da nadin da fatan Allah ya yi yi masa jagora a game da al amari kuma ya zaunar da kasar lafiya baki daya.
Alhaji Yusuf Dauda dai ya gode wa Sarkin Kofa bisa wannan nadi da ya yi masa, yana mai cewa, babban karamci ne a gare, wanda kuma a ya ce zai yi iyaka kokarinsa ya ga ba wa marada kunya.