Yusuf Shuaibu" />

An Nemi A Hukunta Wanda Ya Kashe Matashi Saboda Budurwa

Iyalan Olaitan Balogun sun fada cikin zaman makoki, bayan da abokinsa Olumuyiwa Ajibade, ya dunga dukan sa har sai da ya mutu a rukunin gidaje mai lamba 1 da ke yankin Ajuwon cikin Akuta ta Jihar Ogun. Majiyarmu ta labarta mana cewa, Ajibade ya samu rashin jituwa da budurwarsa mai suna Titi, wacce take yankinsu, sai ya nemi ya kyale ta na wasu watanni, shi kuma Balogun yana da shago a yankin, inda wanda budurwar take yawan kai cajin waya duk lokacin da babu wata a yankin, maigadin rukunin gidajen Kazeem ne ya kai wa Ajibade wannan labarin.
Lokacin da Ajibade ya fara zargin Balogun yana soyayya da Titi a fakaice, a ranar Juma’a 15 ga watan Maris yana tare da masoyiyarsa a ciki gidansa tube, sai ya fara dukan sa har sai da ya mutu. Bidiyon lamarin ya nuna yadda mamacin yake tsirara lokacin da yake dukar sa har sai da ya mutu.
Yayar mamacin mai suna Bosede Olusola, ta bayyana cewa budurwar Balogun Omolara Lawal ta ziyarce shi a ranar da lamarin ya auku, amma lokacin da ta samu ya mutu, ta ga Titi inda ta Omolara ta amince da ta kwana a wurinta. Ta kara da cewa, Balogun yana kan hanyarsa ta fita daga rukunin gidajen bayan ya je ya kai Omolara zuwa gidan su Titi, lokacin da Ajibade tare da abokanansa suka farmaki shi ba tare da sun bar shi ya yi musu bayani ba. matar ‘yan kasuwa ta ci gaba da cewa, “Ajibade da Titi sun samu rashin jituwa a gidan da ta kama haya mai lamba 1 da ke ‘Donald Estate’ a yankin Ajuwon cikin Akute. Gidan yana kusa da shagon Balogun. “Domin haka, a ranar da lamarin ya auku, masoyiyar Balogun, Omolara ta ziyarci shi inda dare ya yi mata. Lokacin da ta yi lattin zuwa gida, sai Balogun ya ga Titi inda ya bukaci Omolara ta kwana a wurinta.
“Ba tare da Balogun ya sani ba, sai maigadin rukunin gidajen mai suna Kazeem ya sanar wa Ajibade cewa, Balogun yana soyayya da masoyiyarsa. A wannan dare, Ajibade tare da abokanansa suka bi Balogun lokacin da yake kan hanyarsa ta fita da rukunun gidajen, sai suka fara dukan sa. “Sun shake masa wuya, inda suka yadda shi a kasa tare da ji masa rauni. Ba su bar shi ya yi bayanin cewa ya kai Omolare ne ta kwana a gidan budurwarsa. “Lokacin da suka fahimci cewa Balogun ya kusa mutuwa, sun garzaya da shi zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Ajunwon, inda Ajibade ya bayar da rahoton cewa ya kama shi ne yana lalata da uwar ‘ya’yansa. Amma lokacin da jami’an ‘yan sanda suka lura cewa Balogun ya daku, inda suka tilasta wa Ajibade a kan ya tsaya, sun ji gaggawar kai shi asibitin Tamara inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar sa.”
Matar Balogun mai suna Modupeola tana neman adalci a kan mutuwar mijinta, ta bayyana cewa lokacin da ta ziyarci asibitin Tamara domin duba shi, likita wanda yake duba shi ya bayyana mata cewa ya mutu sakamakon zubar jini. Matar mai shekaru 34 tana da yaro guda uku ta ce, “Karshen ganin ta da shi tun ranar Juma’a lokacin da zai je shago, ina cikin gida lokacin da Chidi ya zo gida tare da bayyana min cewa, wani yana dukan mijina har sai da aka tafi da shi zuwa asibiti.
“Loklacin da na isa asibiti domin duba mijina, ba zan iya magana da shi ba sakamakon yana cikin mawuyacin hali. Ina ga ana masa allura, inda na yi mamakin yadda aka buge shi har sai da aka kawo shi asibiti. Kansa ya fashe inda daga baya likita ya bayyana mutuwar sa sakamakon rasa jini da ya yi. Ina bukatar gwamnati ta taimake ni wajen gurfanar da wadanda suke da hannu a mutuwar sa a gaban kuliya.”
Kanuwar Balogun mai suna Ifeoluwa Ojo, ta bayyana cewa an kai gawarsa zuwa dakin ijiye gawarwaki da ke asibiti bayan an tabbatar da mutuwar sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa rundunarsa ta cafke Ajibade, bisa zargin sa da bugun Balogun har sai da ya mutu lokacin da ya fadu da shi a wurin masoyiyarsa cikin tsakiyar dare. Oyeyemi ya kuma ce, Ajibade yana zargin Balogun da yin lalata da masoyiyarsa Titi, lokacin da aka tambayi budurwar, sai ta musanta lamarin. Kakakin rundunar ‘yan sanda ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandar Jihar Ahmed Iliyasu, ya bayar da umurnin a mika lanarin gas ashen rundunar ‘yan sanda masu binciken laifin kisa domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfamafar da wanda ake zargi a gaban kuliya. Oyeyemi ya ce, za a mika wanda ake zargi zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Exit mobile version