Connect with us

SIYASA

An Nemi Abdulrasheed Maina Ya Fito Takarar Gwamnan Jihar Borno

Published

on

Al’ummar jihar Borno mazauna jihar Kaduna sun nemi tsohon shugaban hukumar gyara da tsaftace harkar Fansho na Nijeriya, Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina da ya fito takarar Gwamnan jihar Borno a zaben da ke tafe a shekarar 2019.
Shugaban kungiyar, Malam Mustapha Bukar ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da wakilimu a gidansa da ke Kaduna.
Bukar ya bayyana cewa Abdulrasheed Maina na taimakawa al’ummar jihar ta fannnoni da daman gaske. Ya ce lokacin da Maina din ya ke rike da mukami ya samarwa matasan jihar ayyuka a wurare da daman gaske na ma’aikatun gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce lokacin da al’ummar jihar suke fuskantar tashin hankalin ‘yan kungiyar Boko Haram, Maina ya bi garuruwan da al’ummar da ke gudun hijira, in da ya tallafa musu da kudade da kuma kayan masarufi da tufafi.
Malam Mustapha Bukar ya ce ba jihar su ta Borno ba kawai, Nijeriya da Afirka sun alfahari da gogewa da kuma kwarewa irin ta Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina ta fuskar aiki da kuma tallawafa al’umma da sauransu.
Ya ci gaba da cewa, Malam Maina ya kawo gyara sosai a harkar fansho a Nijeriya. Ya ce kafin kwamitin Maina ya gyara harkar fansho a Nijeriya, masu karbar fansho na fama da matsaloli sosai wajen karbar kudaden su na fansho. Amma tunda Maina ya yi gyara a bangaren, ba a kara samun matsala ba a harkar fansho a Nijeriya.
Ya ce idan aka zabi Abdulrasheed Maina a matsayin Gwamnan jihar Borno, al’ummar jihar za su yi bankwana ta talauci da kuma rashin tsaron da ake fama da shi a jihar.
Ya ce duk da ba yanki daya suka fito da Abdulrasheed Maina ba, ya san irin gogewar da Maina ke da ita a fannin mulki za ta taimaki jihar ta Borno. Mustapha Bukar, ya ce shi mutumin arewacin jihar Borno ne kuma Abdulrasheed Maina mutumin kudancin jihar ne.
Ya ce mutanen kudancin jihar ba a taba basu dama sun mulki jihar ba, don haka ya ce wannan lokaci ne da ya kamata a baiwa mutanen kudancin jihar su zama Gwamna don ganin irin rawar da za su taka wajen ciyar da jihar gaba.
Daga nan Mustapha Bukar ya yi kira ga Malam Abdulrasheed Maina da ya amsa kiransu ya fito takarar Gwamnan jihar don kawo ci gaba mai ma’ana a jihar baki daya.
Mustapha Bukar ya yi kira ga al’ummar jihar da su baiwa tafiyar Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina goyon baya don ganin ya lashe zaben da za a yi a shekarar 2019.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: