Connect with us

SIYASA

An Nemi Abubakar Ya Fito Takarar Gwamnan Katsina

Published

on

An nemi Malam Abubakar Isma’ila Isa Funtuwa da ya fito takarar Gwamnan jihar Katsina a zaben da ke tafe a shekarar 2019.

Gamayyara kungiyoyin siyasa masu goyon bayan Abubakar din ne dage yankin Kadaduwa ne suka yi wannan kiran lokacin da suke zantawa da manema labarai a Funtuwa.

Kungiyoyin, wadanda ke karkashin jagorancin Alhaji Sani Karau-Karau Mahuta, sun bayyana cewa jihar Katsina na cikin wani hali na rashin tabbas sakamakon tashin iya mulki na gwamnati mai ci yanzu.

In da suka ba da misali da cewa Gwamnatin ta hana ma’aikatan Kananan Hukumomi ma su tarin yawa albashinsu na sama da shekaru biyu. Don haka iyalan ma’akatan na cikin halin kunci da rashin tabbas a rayuwa. Don haka suka bayyana cewa gwaninsu, Malam Abubakar Isma’ila Isa zai tabbatar da adalci da kuma baiwa kowa hakkinsa idan ya zama Gwaman jihar Katsina.

Alhaji Sani Mahuta ya ci gaba da cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta yi wani shiri ba na raba takin zamani a wannan shekarar duk da cewa tuni damina ta yi nisa. Ya ce wannan rashin iya mulki ne na masu mulki a jihar. Don haka ya ce gwaninsu idan ya zama gwamna zai tabbatar da cewa takin zamani ya isa ga manoma tun a watan hudu.

Ya ce manufofin Abubakar na taimakon al’umma ne da kuma kawo sauyi mai ma’ana a jihar ta Katsina. Don haka ya ce za su ci gaba da rokon Malam Abubakar Isma’ila Isa har sai ya amince da bukatarsu ta yin takarar Gwamnan jihar.

Sani Mahuta ya kara da cewa, idan gwaninsu ya amince da yin takarar Gwamnan. Za kuma su shiga lungu da sako na fadin jihar don tallar manufofinsu ga al’ummar jihar.

A karshe ya bayyana cewa a shirye suke don ganin sun kawar da gwamnati mai ci yanzu a jihar don kawo sauyin da zai amfanar da al’ummar jihar ta hanyar kawo ci gaba mai amfani da kuma bai wa kowa hakkinsa.

Advertisement

labarai

%d bloggers like this: