Bala Kukkuru" />

An Nemi Al’ummar Hausawa Mazauna Legas Da Su Rika Taimakon Juna

Wani Bahaushe mazaunin jihar Legas mai suna Shugaba Mahammadu Arugungu wanda yake gudanar da kasuwancinsa a labintis karkashin gadar unguwar marin bic ta karamar hukumar Apapa ya ummurci al’ummar Hausawa da sauran kabilun arewacin Nijeriya mazauna Legas da su rika taimakama ‘yan uwansu. Shugaba Mahammadu Arugungu ya yi wanan bukatar ne jim kadan bayan tashinsu daga taron da ya kira na al’ummar Hausawa da sauran kabilun arewacin Nijeriya mazauna Apapa a cikin garin Legas domin tattaunawa bisa ga matsalolin dake damunsu tare da bayar da shawarwari akan abubuwan da za su kawo masu hadin kai da zaman lafiya da tai makon yan uwansu bakidaya

Ya cigaba da cewa wajibinsu ne da sauran kabilu mazauna wannan unguwa idan har suna bukatar su kara samun cigaba ta fannin kasuwancinsu da sauran al’ammuran da suka shafi rayuwarsu a wajen ubangiji sai sun koma ga Allah su kuma sauyama na kasansu tare da taimakon junansu, ya cigaba da cewar akan haka yake sha’awartar al’ummar Hausawa mazauna wannan jihar ta Legas da sauran kabilun arewacin Nijeriya dasu cigaba da taimakon junansu tare da tausaya ma na kasansu domin samun wadannan bukatu nasu a wajan ubangiji. Sannan ya cigaba da cewar yana mai jajantawa al’ummar jihar Legas da Nijeriya da duniya baki daya agame da bullowar wannan annobar ta cutar korona data addabi al’ummar Nijeriya da sauran kasashen duniya.

Ya kara da cewa, yana mai shawartar al’ummar Nijeriya musamman a wannan lokaci da su cigaba da bin dokokin da Gwamnati ta shinfida domin kauce wa kamuwa da wannan cuta ta kurona a fadin kasar nan tare da dakile yaduwar ta a kasar ta Nijeriya.

Ya kara da cewa, idan har al’ummar Nijeriya suka bi wadannan dokoki da Gwamnati ta shinfida domin kauce wa kamuwa da wannan cutar ta kurona suma sun ba Gwamnati tasu gudummar a wannan dangare a kokarin Gwamnati na kare lafiyar al’umma

Ya kuma cigaba da cewa, tunda Gwamnatin tarayya da sauran Gwamnatocin jihohin kasar nan suna yi iyakar kokarinsu a wajen kashe makudan kudade tare da ba al’umma shawarwari domin kare lafiyarsu daga kamuwa da wannan cutar ta kurona da cutut tukan da suke yawo adoran duniya baki daya

Exit mobile version