Khalid Idris Doya" />

An Nemi EFCC Ta Binciki Yadda Aka Raba Tallafin IIRO Ga Marayu A Bauchi

An bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da kuma (ICPC) su bincikin yadda a ka raba tallafin da hukumar bada agaji ta kasar Saudiyya ta bai wa wadansu yara marayu da marasa galihu a jihar Bauchi, domin ba su tallafi a kan gudanar da iliminsu.

Wannan kiran na zuwa ne bayan da korafe-korafe su ka fara tasowa kan yadda hukumar da ke kula da marayu da marasa galihu a jihar take rabar da kudaden tallafin da aka baiwa marayun.

Kungiyar mata masu wayar da kai kan dimukradiyya da zama lafiya su ne suka yi wannan kira ga EFCC da ICPC na su binciki yadda aka rarraba wadanan kudade a wani taron manema labarai da suka yi a Bauchi.

Daraktan kungiyar Addaji Muhammad ta shaida cewa; “wannan tallafi kungiyoyi masu zaman kansu ne su ka nemo ba gwamnati ba; kuma da a ka kawo tallafin sai aka ki a kira kungiyoyin da suka yi hanyar samun tallafin, sannan wasu daga cikin marayun sun koka wa kungiyar kan cewa ana basu kudade daban-daban wasu naira dubu 18, zuwa dubu 400 amma mutum biyu ne kawai suka samu naira dubu 400 saura sai dubu 20, 30 wasu zuwa dubu 70 har ma da mai dubu 118,” Inji Ta.

“Sannan kuma wani karin matsalar ma, koda mutum yana cikin kaso na kaza to ba zai samu cikakken kudin ba, misali mai naira dubu 118 sai ka ga kila naira dubu 100 za a bashi, wai an cire kashi goma sha uku cikin kudin a hukumar gwamnati ta BASOBCA,” Kamar yadda ta shaida.

A bisa wannan ne suke roki hukumomin  yaki da cin hanci da rashawa na Nijeriya da su binciki yadda aka bada wannan tallafi da yadda ake rabarwa.

Binciken wakilinmu ya nuna cewa tun cikin shekara ta 2008 ne wata kungiyar tallafawa mata da marayu da marasa galihu  mai suna (Support Initiatibe for Bulnerable Children) ‘SIBWoC’ tare da hadin guiwar wata kungiyar tallafawa marayu mai suna ‘Angarar Yuguda’ suka yi kokari don samar da tallafi wa yara Marayu da Marasa Galihu ta fuskar kula da lafiya, Ilimi, matsuguni, tallafawa iyalan da basu da karfi da kuma tallafi ta fuskar shari’a da kuma sauran fannonin da zasu inganta rayuwar dan adam da yanayin zamantakewar rayuwarsa.

Cikin wata takarda da Hajiya Baheejah Mahmood wacce ita ce Darakta na kungiyar Angarar Yuguda da kuma Kabiru Labbo wanda Shine Sakatare na SIBWoC suka sanya hannu akai wanda suka aikawa da kwafinta ga Daraktan kafa hukumar bada tallafi wa marayu da marasa galihu na jihar Bauchi ba wato (Bauchi state Orphans and Bulnerable Children Agency), (BASOBCA) wanda wakilinmu ya samu kofin takardar; ta ci gaba da cewa  wadannan kungiyoyi suna samar da tallafi ne wa marayu da marasa galihun da aka tantancesu ta hannun gwamnatoci, hukumomin bada agaji, dake ciki da wajen kasar nan don su tallafawa ire-iren wadannan marayu da marasa galihu a cikin da wajen kasar nan.

“Cikin shekarar ne kungiyoyin suka yi ta kai ziyara ofishin hukumar bada agaji na kasa da kasa na kasar Saudiyya   dake da ofishi a Kaduna, wato International Islamic Relief Organisation (IIRO) daga nan sai hukumar ta yi sha’awar tallafawa ire-iren ayyukan da kungiyoyin suke gudanarwa. Inda suka fahimci juna kan cewa kungiyoyin zasu samar da filin da za a iya gina masallaci a kuma samo wadanda zasu ci moriyar shirin musamman wadanda ke neman tallafi ta fuskacin ilimi,” A cewar takardar.

Suka kara da cewa; “Dangane da haka sai wadannan kungiyoyi suka kai ziyara dukkan lunguna da sakona na jihar Bauchi da nufin samar da fili ko ta hannun gwamnati ko kuma al’ummar dake da niyyar bada filin saboda Allah. sannan kungiyoyin sun tantance ire-iren matsalolin al’ummar domin gano tallafin da suka fi bukata.

“Sakamakon haka   ita kuma hukumar bada agaji na IIRO ta gina Masallatai guda 19 a cikin jihar Bauchi, kuma aka zakulo yara daga yankunan kanana hukumomi 20 dake Bauchi masu bukatar tallafin, kungiyoyin ne suka dauki nauyin kawosu Bauchi daga yankunasu  don a yi musu rijista,” A cewar bayanin.

Sun ce a lokacin da Jami’an kungiyar IIRO suka je Bauchi sun shafe makonni biyu suna yin rijistar wadannan kungiyoyi sune rika dauki dawainiyar yin dukkan ayyuka, “mun kashe kudade sama naira Miliyan Biyu da dubu dari uku. An kashe kudaden ne wajen sufuri, abinci, daukar hotuna da kuma samar da dukkan kayayyakin da ake bukata,” A cewar su.

Kungiyoyin suka ce a lokacin da suke ci gaba da bin sahun lamari sai suka riski tallafin ya shiga hanun wasu daban, “Muna son mu fayyace gaskiya lokacin da aka fara wannan yunkuri ba a ma kafa hukumar bada tallafi wa Marayu da Marasa Galihu na Jihar Bauchi ba wato (BASOBCA),” Inji su.

A cikin takardar sun roki hukumar BASOBCA da su bar wadannan kungiyoyi su karasa wannan aiki don gudun kar a samu kuskure ko a karkatar da tallafin kamar yadda suke samun koke daga mutanensu cewa ana ciccire sunayen wadansu marayun ana sauyasu da wasu.

Daga bisani Hajiya Bahijja wacce ta taba shugabancin hukumar BASOBCA a mulkin Yuguda ta sha alwashin neman hakkinta a kotu domin a cewarta marayu da marasa galihu da dama suna kawo mata korafi da kokensu Kan matsalolin da suka Sanu, kana ta shaida cewar sun yi rijista was marayun da za su ci gajiyar wannan shirin amma wasu har yanzu babu sunanzu a ciki.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin shugaban hukumar kula da marayu da marasa galihu na jihar Bauchi kan zarge-zargen da aka musu hakan ya citura, amma idan muka sami karin bayani daga garesu za ku ji nasu bangaren.

Exit mobile version