An Nemi EFCC Ta Hada Hannu Da NDLEA Wajen Dakile Shan Miyagun Kwayoyi

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

kungiyar mata, matasa, yara da dakile aikata laifuka, wata kungiya mai zaman kanta, ta nemi goyon bayan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a kan duba shan miyagun kwayoyi da fataucinsu.

Dakta Farida Waziri, wacce ta kafa kungiyar, ta yi wannan maganar ne a yayin ziyarar girmamawa da ta kai wa hedikwatar NDLEA a ranar Laraba a Abuja.

Waziri, tsohon shugaban EFCC, ya ce, irin nasarorin da hukumar ta NDLEA ta samu a cikin watanni hudu da suka gabata abin a yaba ne.

“Abin birgewa ne kuma abin a yaba ne yadda shugaban, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya sauya fasalin NDLEA da yaki da shan kwayoyi da fataucin mutane. Muna yabawa da hazikin, da dabi’u da dabarun da ke ingiza sabuwar NDLEA din,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa, “a cikin kungiyar, muna yabawa da wannan kokarin sannan kuma mun sami wuraren da suke da sha’awa a cikin sabon ci gaban a NDLEA. Na farko shi ne shirin bayar da shawarwari na hukumar, yanki wanda zai iya amfanar da ita ga NDLEA kuma daya daga cikin abubuwan da muke gabatarwa.”
“Sabon shugabanci a hukumar ta NDLEA ya kalubalanci al’umma da su tashi haikan wajen hana shan miyagun kwayoyi, kuma kungiyoyi da dama tun daga lokacin sun saurari wannan kira. Ba ma son a bar mu a baya, kungiyar na da sha’awar dakile shan miyagun kwayoyi. Muna da tsare-tsaren da za mu shirya wajen bayar da labarin yadda zai dace da ranar 2021, ta ranar yaki da shan miyagun kwayoyi,” in ji shi.

Ta kara da cewa, “taron na da niyyar gabatar da mutane kamar wadanda aka yiwa garambawul a harkar shan miyagun kwayoyi, iyaye, yara da matasa don bayar da bayanan abubuwan da suka faru a baya game da shan miyagun kwayoyi. A shirye muke da mu hada hannu da NDLEA, saboda ganin cewa babban zaben 2023 ya gabato, lokaci ya yi kusa da mu,” in ji ta.

Da yake mai da martani, Marwa ya yaba wa Waziri bisa kafa kungiyar.
Marwa ya ce, kasar na fuskantar kalubalen amfani da kwayoyi.

“Mun bayyana kuma har yanzu muna tsaye a kai don gudanar da gwajin kwayoyi ga ‘yan siyasa, dalibai da sauran jami’an gwamnati. Ba za ku iya ba da amanar rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya a hannun mutanen da kawunansu bai mike ba saboda amfani da kwayoyi,” in ji shi.

Ya ce, “Ina so in yi amfani da damar in ce, wa’adi ya hau kan dukkan ‘yan Nijeriya don fuskantar wannan kalubalen. Ina so kuma in nemi kungiyar da ta magance matsalar nuna kyama, musamman a kan mata masu matsalar shaye-shaye, da sanin cewa suna bukatar taimako amma saboda tsoron kyamar.”
“Haka zalika, tarbiyyar yara tana da matuaar muhimmanci. Dole ne ya fara daga matakin farko. Ina da yakinin cewa nan ba da dadewa ba za mu samu sauki daga matsalar da kasar ke fama da shi” in ji shi.

Exit mobile version