Abdullahi Sheme" />

An Nemi Gwamnati Ta Daure Da Ta Bude Makarantun Kasar Nan

Makarantun Kasar Nan

An yi kira ga Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa  Alhaji Muhamdu Buhari da ta daure ta bude manyan makarantun kasar nan wadanda suke a karkashinta domin cigaban kasar nan wannan kiran ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar manoma da sayar da hatsi da hudda da kamfanoni na kasa reshen jihar Katsina, Alhaji Isa Balarabe Bilbis kuma shugaban kungiyar ‘Amana Farmers Growers Association of Nigeria  AFGASAN’  na jihohin Arewa maso yamma.

Alhaji Bilbis ya cigaba da cewa, kiran ya zama wajibi ganin yadda aka kwashe sama da wata 10 ba tare da komawar yara makaranta ba ya ce rashin karatun ba karamin illa bane musamman ga matasan kasar nan duk da daukar dogon lokacin da kungiyar malaman makarantun jami”a suka yi watau ASUU  sai daga bisani suka janye yajin aikin saikuma ga dawowar cutar kurona, Alhaji Isa ya ce yana ba Gwamnati shawara yakamata ta samar da mahimman matakan kara kare kawunan al’umma don a cigaba da amfani dasu domin bude makarantun   zaman kashe wando da yaran ke yi ya yi yawa a halin yanzu dukkan yaran makarantar tun daga na firamare da gaba da firamare har ‘yan jami”ia suna gidajensu wannan abin takaici ne kwarai, Alhaji Balarabe ya ce Allah ya kawomu sabuwar shekara don haka yana kira ga Gwamnati da ta dauki sabbin matakai na kawo karshen rashin tsaron da ya addabi jama”armu kusan kullum sai an kashe mana mutane ko  daukesu ayi garkuwa dasu dan neman kudin fansa ya ce a shekarar da ta wuce amsami asarar rayuka da asarar dukiya ta wajen sace shanum al’umma da biyan kudin fansa a wasu wurare noma ya gagara koma kwashe amfanin gona.

Exit mobile version