Matukar ana son a kawar da matasan kasar nan daga aikata miyagun aikace aikace musamman yadda aka yi amfani da su wajen tayar da hargitsi sakamakon kawo karshen End-SARS inda faga ta rikede ta zama tarzoma da kone kone har takai ga asaran rayuka da dukiyoyin al’umma.
Babu abin da ya kawo haka sai rashin aikin yi ga matasan sannan da yawa daga cikin su sun kammala karatu amma babu aikin yi. Kan haka ya zama wajibi gwamnati ta taimakawa masu masana’antu da ingantacen hasken wutan lantarki wanda al’umma za su samu aikin yi musamman matasa.
Wannan bayanin haka ya fito ne daga bakin Alhaji Kabiru Shitu, alokacin da yake zanatawa da manema labarai a birnin Kano, Alhaji Kabiru Shitu ya ce yawancin tashe tashen hankula da suke faruwa yanzu haka akasar nan rashin aikin yin a daya daga cikin abin da suke haifara da su.
Malam Kabiru Shitu, da ke zaune a unguwar Gwamaja cikin birnin Kano, ya ce gwamnati ta mayar da hankalin ta sosai wajen daukar aiki ga matasan, tare da bude wuraren koyar da sana’oin dogaro da kai, matukar ta yi haka matasa ba za su amince ayi amfani da su wajen tayar da hargitsi bada yardar Allah.
A matsayin shi na dankasuwa ya yi kira a garesu da su sanya tsoron Allah a cikin hurdodin kasuwancin da suke yi da al’umma, sannan har ila yau su kasance suna taimakawa masu karamin karfi, ganin halin da ake ciki na matsin rayuwa
Daga karshe ya yi kira ga iyayen yara da su kara kula sosai akan kula da tarbiyar yaran su, tare da tabbatar da cewa suna zuwa makaranta da kuma sanin su wa suke hulda da su.
Fitaccen Dan Jarida A Duniya, Larry King, Ya Rasu
Fitaccen mai watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo, Larry King, wanda...